Toni Anenih, daya daga wadanda su ka kyankyashi PDP ya mutu
- Tony Anenih, tsohon ministan aiyuka kuma daya daga cikin wadanda su ka kafa jam'iyyar PDP a shekarar 1998, ya mutu
- Shafin adana bayanai na Wikipedia ya nuna cewar an haifi Mista Anthony Akhakon Anenih a Uzenema-Arue ta garin Uromi da yanzu ke jihar Edo ta yanzu
- Anenih, mai shekaru 85, ya mutu ne a asibitin Cedarcrest da ke Abuja, inda ya ke samun kulawa a kan wata cuta da ba a bayyana ba
Tony Anenih, tsohon ministan aiyuka kuma daya daga cikin wadanda su ka kafa jam'iyyar PDP a shekarar 1998, ya mutu.
Anenih, mai shekaru 85, ya mutu ne a asibitin Cedarcrest da ke Abuja, inda ya ke samun kulawa a kan wata cuta da ba a bayyana ba.
Shafin adana bayanai na Wikipedia ya nuna cewar an haifi Mista Anthony Akhakon Anenih a Uzenema-Arue ta garin Uromi da yanzu ke jihar Edo ta yanzu.
Ya yi karatun makarantar firamare da sakandire a Benin, babban birnin jihar Edo, kafin daga bisani ya wuce zuwa makarantar horon 'yan sanda da ke Ikeja a jihar Legas, daga inda aka zabe shi zuwa wata makarantar horon 'yan sanda a Basingstoke, kasar Ingila.

Asali: Facebook
Ya yi aiki a matsayin Malamin da ke horar da 'yan sanda a makarantun 'yan sanda da dama kafin ya yi ritaya a mukamin kwamishina.
Anenih ya zama shugaban jam'iyyar NPN mai mulkin kasa daga shekarar 1981 zuwa 1983.
DUBA WANNAN: Bana jin ko da magudi APC za ta iya cin zaben 2019 - Jigo a jam'iyyar
Daga baya Anenih ya zama shugaban jam'iyyar SDP da MKO Abiola ya ci zaben shekarar ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.
Bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, Anenih ya kasance daya daga cikin 'yan siyasar da su ka gina jam'iyyar PDP da ta samar da Obasanjo a matsayin shugaban kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng