Magoya bayan Buhari sun lissafo kokarin da Gwamnatin sa ta ke yi
- Sanatan Katsina Abu Ibrahim yace ba a fadawa Duniya irin kokarin da Buhari yayi musamman a bangarorin tsaro da sufuri da tattalin arziki
- Kungiyar Buhari Youth Organisation (BYO) ta Matasan da ke goyon Shugaba Buhari sun ce gidajen yada labarai ne ba su aikin da ya dace a Kasar nan
- Shugaban Kungiyar BYO na Legas Abdulwaheed Odunuga yace Shugaba Buhari ya cika manyan alkawuran da ya dauka lokacin neman zabe

Asali: Facebook
Kungiyar nan ta Matasan da ke goyon bayan Shugaban kasa Buhari watau BYO ta bayyana cewa Ubangiji ne ya aikowa Najeriya mutum mai daraja da kima irin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma yayi abin a yaba masa.
Wannan kungiya tace gidajen yada labarai ba su aikin da ya kamata wajen yada ayyukan Gwamnatin Shugaba Buhari. Kungiyar tace Shugaba Buhari ya cika alkawarin da yayi na yaki da cin hanci da inganta tsaro da bunkasa tattali.
KU KARANTA: Duk alkawuran da na dauka na cika su yanzu – inji Shugaban kasa Buhari
Sanatan APC Abu Ibrahim wanda yana cikin Dattawan wannan Kungiya ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya yi matukar kokari musamman wajen gyara hanyoyi da kuma inganta tsaro da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Abdulwaheed Odunuga wanda shi ne Jagoran wannan Kungiya a Jihar Legas ya jinjinawa kokarin Shugaba Buhari. Shi ma dai Shugaban BYO a Najeriya Yusuf Nalado yace an samu canji a bangaren harkar noma a Najeriya.
Yetunde Babajide wanda tana cikin manyan Magoya bayan Buhari a Kasar Yarbawa ta bayyana cewa ya kamata mutanen Najeriya su sake zaben Buhari a 2019 domin cugaba da aikin da ya fara na dora kasar nan a kan turbar gyara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng