Zan rushe Gonin Gora gaba daya idan za su dinga tayar da hankalan jama’a - El Rufa'i

Zan rushe Gonin Gora gaba daya idan za su dinga tayar da hankalan jama’a - El Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi rantsuwar daukar tsatsaran mataki akan matasan Gonin Gora kan ci gaba da tayar da hankulan jama’a da suke yi a jihar Kaduna.

A cewar gwamnan zai rushe garin gaba daya a mayar da shi fili, domin a cewar sa ba zasu zuba idanu suna kallon wasu yan tsirarun mutane da haifar da bala’i a jihar ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin jama'ar jihar Kaduna a cikin shirin Hannu da yawa na gidan Rediyon tarayya na Kaduna da ake gabatarwa yanzu haka kai tsaye akan halin da tsaro ya ke ciki a jihar Kaduna tun bayan sanya dokar hana walwala a fadin Jihar.

Zan rushe Gonin Gora gaba daya idan za su dinga tayar da hankalan jama’a - El Rufa'i
Zan rushe Gonin Gora gaba daya idan za su dinga tayar da hankalan jama’a - El Rufa'i
Asali: Facebook

Ya ce: "Wallahi Tallahi na rantse da Allah Ubangijina matukar Matasan Gonin Gora za su cigaba da kawo mana tashin tashina a jiharmu ta Kaduna, to zan rushe wannan gari gaba daya in mayar da shi Fili, domin ba zamu zuba ido wasu tsiraru na haifar mana da matsala suna jefa Jama'a cikin halin tsoro ba, babu wanda ya fi karfin gwamnati".

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaban APC a Enugu ya tsallake rijiya da baya yayinda makasa suka harbi mai tsaronsa

Gwamnan El Rufa'i ya tabbatar da cewar baya cikin Kaduna a ranar da hargitsi ya tashi yana Abuja, kuma cikin gaggawa ya yanke abinda yake ya nufo Kaduna, akan hanya ne ya ga cunkoson motoci ya tambaya aka ce mishi matasa ne suka tare hanyar Gonin Gora, haka ya fito ya nufi wurin Matasan na ganin shi suka gudu, akabi aka kamo su suna hannu a halin yanzu.

Ya kuma bukaci dattawan yankin su dauki matakin dakile Matasan yankin aikata haka, idan kuma ba su hanu ba wallahi za su gamu da fushin gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng