Rikicin Kaduna: An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kachia

Rikicin Kaduna: An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kachia

- An sassauta dokar hana fita a garin Kachia da ke Jihar Kaduna

- Al'umma Kachia za su iya fara harkokinsu daga karfe 6 na safiya zuwa 5 na yamma

- Majalisar Tsaro na jihar ta ce an sassauta dokar ne saboda biyaya da doka da al'ummar yankin ke yi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirgan a karamar hukumar Kachia kamar yadda sanarwa ta fito a safiyar yau daga bakin mai taimakawa gwamnan jihar a fannin yada labarai, Samuel Aruwan.

Rikicin Kaduna: An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kachia
Rikicin Kaduna: An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kachia
Asali: Facebook

Aruwan ya bayyana cewa Majalisar Tsaro na Jihar Kaduna ta yi la'akari da yadda al'ummar Kachia suka kasance masu biyaya da da'a da doka duk da cewar suna cikin juyayi da dimuwa na rashin basareken yankin, Agom Adara.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Wannan biyaya da da'a ga doka ne yasa Majalisar Tsaro na Jihar ta bayar da umurnin sassauta dokar hana fita a Kachia daga yau Asabar 27 ga watan Oktoban 2018.

Ya kara da cewa mutanen garin za su iya cigaba da harkokinsu daga yanzu har zuwa karfe 5 na yamma.

Daga gobe kuma Lahadi 28 ga watan Oktoba, mutanen garin Kachia suna da damar fara harkokinsu daga karfe 6 na safiya zuwa karfe 5 na yamma.

Majalisar Tsaron ta ce sauran sassan jihar Kaduna za su cigaba da kasancewa karkashin dokar na hana fita na sa'o'i 24 har sai lokacin da Majalisar tayi nazarain matakin sassauta dokar a sauran wurare.

Sanarwar ta ce an sanya dokar ne domin kare rayukkan al'umma ba domin a musguna musu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164