Yadda jami'an civilian JTF suka taimaka wajen kawo karshen rikicin Kaduna
Mazauna jihar Kaduna sun yaba da irin na mijin kokarin da jami'an sa kai na Civilian Joint Task Force (JTF) da akafi sani da 'yan kato da gora su kayi wajen kawo karshen rikicin da ya barke a wasu sassan jihar ta Kaduna.
An gano cewar 'yan kato da gora sun mamaye manyan tittuna garin yayin da rikicin ya barke a jihar tun ranar Lahadi da ta gabata.
Daily Trust ta gano cewar jami'an JTF din sun raba kawunansu a unguwanin da ake zargin rikici zai iya barkewa kamar Rigasa, Tudun Wada, Sabon Gari, Kakuri, Kawo, Jaji, Sabon Tasha da sauransu.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa
Majiyar Legit.ng ta gano cewar yayin da rikicin ya barke, 'yan kato da gora ne suka hana wasu fusattatun matasa tare tittunan mota domin kashe fasinjoji da basu san hawa ko sauka ba.
Wani mazaunin Kakuri mai suna Samaila ya shaidawa Daily Trust cewar 'yan JTF din ne suka tabattar da zaman lafiya a unguwanni yayin da rikicin ya barke.
"A gaskiya bana daukansu da muhimmanci a baya amma yanzu ina matukar ganin girmansu saboda yadda suka tabbatar da zaman lafiya a unguwar mu.
"Su ne suka taka wa kangararrun yaran unguwa birki domin kada su tayar da fitina a unguwanni," inji shi.
Wani mazaunin Tudun Wada mai suna Bello Idris ya ce "Wasu matasa sunyi yunkurin kona wajen bauta amma 'yan kato da gora ne suka taka musu birki, sun fattatake su har sai da suka gudu," inji shi.
A cewarsa, ya kamata gwamnatin jihar ta karfafa musu gwiwa domin suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng