Sharbar romon dimukradiyya: Muhimman ayyuka 6 da jama’an Jigawa suka karu dasu a gwamnatin Buhari

Sharbar romon dimukradiyya: Muhimman ayyuka 6 da jama’an Jigawa suka karu dasu a gwamnatin Buhari

Masu iya magana na cewa don samun lada ake yin Sallah, kuma dama ai ladar siyasa a duniya ake samunta, musamman idan jama’a suka jajirce suka baiwa dan takarar da suke kauna dimbin kuri’un da suka kai shi ga nasara, ya zama wajibi ya biya su da alheri.

Da wannan ne LEGIT.com ta gudanar da bincike don ganin hanyoyin da al’ummar jahar Jigawa suka ci moriyar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, jahar da ta bashi dubunnan kuri’un da suka kai shi ga samun nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

KU KARANTA: Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin ficewa daga jam’iyyar

Sharbar romon dimukradiyya: Muhimman ayyuka 6 da jama’an Jigawa suka karu dasu a gwamnatin Buhari
Gidajen
Asali: Facebook

Alkalumma sun nuna Buhari ya samu kuri’u dubu dari bakwai da casa’in da saba’in da bakwai, da dari biyu, da arba’in da shida (797, 246) a jahar Jigawa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, yayin da shugaban kasa na wancan lokaci Goodluck Jonathan ya samu kuri’u dubu dari da ashirin da daya, da dari shida da sittin da biyar (121,665) a PDP.

Bugu da kari kananan hukumomin Dutse da Gwaram ne suka fi baiwa Buhari mamakon kuri’u, inda karamar hukumar Dutse ta bashi kuri dubu hamsin da bakwai da dari takwas da tamanin (57,880), ya samu dubu hamsin da bakwai da dari biyu da saba’in da bakwai (57,277).

Sharbar romon dimukradiyya: Muhimman ayyuka 6 da jama’an Jigawa suka karu dasu a gwamnatin Buhari
Gadar
Asali: Facebook

Don haka duba da sahihan alkalumman nan, a iya cewa kwata kwata bai dace a ci yaki da jama’an jahar Jigawa a barsu da kuturun bawa ba, kuma tabbas an yi dace basu tura motar alfa ta badesu da hayaki ba, inda a wasu daga cikin ayyukan da suka mora daga gwamnatin Buhari sun hada da;

- Ciyar da daliban makarantun Firamari kyauta

- Cigaba da aikin gadar sama ta garin Shuwarin

- Aikin fadada hanyar Kano zuwa Maiduguri da ta ratsa Jigawa

- Gyaran hanyar Hadejia-Nguru kashi na biyu, da Kirkikasamma zuwa Nguru

- Gina gidajen gwamnati masu sauki don ma’aikata

- Daukan matasa dubu goma sha hudu da dari hudu da arba’in da hudu (14,444) aikin N-Power

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng