Yadda su Atiku Abubakar da Uche Secondus su ka lallashi Ike Ekweremadu a Jam'iyyar PDP

Yadda su Atiku Abubakar da Uche Secondus su ka lallashi Ike Ekweremadu a Jam'iyyar PDP

- Ike Ekweremadu yayi yunkurin barin PDP bayan Atiku ya dauko Peter Obi

- Mataimakin Shugaban Majalisar yayi tunani shi Atiku zai tsaida Mataimaki

- Yanzu dai Jagororin PDP sun roki babban Sanatan Kasar sun shawo kan shi

Yadda su Atiku Abubakar da Uche Secondus su ka lallashi Ike Ekweremadu a Jam'iyyar PDP
Atiku ne ya hana Sanata Ike Ekweremadu komawa APC
Asali: Depositphotos

Kwanakin baya kadan ne Sanata Ike Ekweremadu wanda yana cikin manyan ‘Yan Majalisar Tarayya a Kasar nan yayi barazanar barin Jam’iyyar PDP. Yanzu mun samu labarin yadda manyan Jam’iyyar s ka lallabe shi ya fasa canza sheka.

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus, da kuma Atiku Abubakar wanda shi ne ‘Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar su ne su roki Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ya hakura ya zauna a PDP.

KU KARANTA:

Jaridar Punch ta rahoto cewa ran Sanatan na PDP ya baci ainun bayan Atiku bai dauko sa a matsayin Abokin takararan sa ba. Sanatan dai ya gama sakin-jiki cewa zai yi takarar kujerar Shugaban kasa da Atiku, kurum sai ya ji an zabi Peter Obi.

Majiyar ta bayayana cewa Shugaban PDP da kan sa da kuma Atiku Abubakar ne su ka roki Ekweremadu yayi hakuri kar ya koma Jam’iyyar APC ya cigaba da zama da PDP domin akwai abin da su ka shirya masa idan an kai ga nasara bayan 2019.

Wasu sun nuna cewa dole Ekweremadu ya ji haushi domin shi yayi wa Atiku wahala a wajen zaben tsaida gwani amma aka zabi tsohon Gwamna Obi. Tuni dai ‘Dan Majalisar wanda ba ya kasar a yanzu ya tabbatar da cewa yana nan daram-dam-dam a PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng