Shugaban kasa ya kaddamar da wani babban aikin gwamnatinsa a jahar Ribas

Shugaban kasa ya kaddamar da wani babban aikin gwamnatinsa a jahar Ribas

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Fatakwal na jahar Ribas da nufin bukatar ya kaddamar da wani gagarumin aiki da aka yi a filin sauka da tashin jiragen sama na Fatakwal, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Wannan katafaren aiki kuwa shine gina sabon titin da jiragen sama ke sauka da tashi akansa, sa’annan aikin ya zama abin tinkaho ne saboda akwai wasu gine gine da suke hade da wannan titi, kamar su dakin jiran fasinja, wajen tantance kaya, dakin bincike, wajen kwasan kaya da sauransu, kuma duk ginin zamani aka yi musu.

KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawwuna: Mace ta zama shugabar wata kasar Afirka a wani yanayi na rabo

Shugaban kasa ya isa jahar Ribas domin kaddamar da wani babban aikin gwamnatinsa
Buhari
Asali: Facebook

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito da misalin karfe 12:20 ne shugaba Buhari ya isa Fatakwal don kaddamar da ayyukan da suka gudana a karkashin sa idon ministan sufurin jirgin sama, Malam Hadi Sirika.

Sai dai wannan aiki gude ne cikin ireirensa guda hudu da za’a gina a filayen sauka da tashin jirage guda hudu a Najeriya, kuma za’ayisu ne da kudin bashi na dala miliyan dari biyar da kasar China ta bayar, inda Najeriya ta bada dala miliyan dari.

Shugaban kasa ya isa jahar Ribas domin kaddamar da wani babban aikin gwamnatinsa
Buhari
Asali: Facebook

A tsarin farko da aka yi ma ayyukan, an shirya za’a kammalasu ne a cikin watanni goma sha takwas, amma sai a yanzu bayan shekara biyar ake kammala na Fatakwal, yayin da ake sa ran na Abuja, Kano da Lagos zas biyo baya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai ministan sufurin jirgin sama, Hdi Sirika da gwamnan jahar Ribasm Gwamna Nyesom Wike da ministan kwadago Chris Ngige..

Shugaban kasa ya isa jahar Ribas domin kaddamar da wani babban aikin gwamnatinsa
Cikin ginin
Asali: Depositphotos

Shugaban kasa ya isa jahar Ribas domin kaddamar da wani babban aikin gwamnatinsa
Cikin ginin
Asali: Depositphotos

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng