An sake maka tsohon Gwamna Sule Lamido a Kotu da laifin satar kudi

An sake maka tsohon Gwamna Sule Lamido a Kotu da laifin satar kudi

- EFCC ta sake komawa Kotu da tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido

- Ana zargin Tsohon Gwamnan na PDP da ‘Ya ‘yan sa da satar kudin Gwamnati

An sake maka tsohon Gwamna Sule Lamido a Kotu da laifin satar kudi

EFCC ta kara taso keyar tsohon Gwamna Sule Lamido
Source: UGC

Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kara maka tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da ‘Ya ‘yan sa a gaban wani babban Kotu a Birnin Abuja.

EFCC na zargin Sule Lamido da aikata wasu laifuffuka har 43 wadanda su ka hada da satar kudin Gwamnati da kuma cin amana da wuce gona da iri. Yanzu dai an shigar da kara ne a gaban Alkali mai shari’a Ijeoma Ojukwu a Unguwar Maitama.

KU KARANTA: An yi kare jini biri jini tsakanin 'Yan daba da 'Yan Sanda a Kano

An maka tsohon Gwamnan na Jigawa a gaban Kotu ne tare da ‘Ya ‘yan sa Aminu Lamido and Mustapha Lamido da kuma wani Bawan Allah mai suna Aminu Wada Abubakar. Sule da sauran wadanda ake zargi dai sun fadawa Kotu cewa su na da gaskiya

Haka kuma daga cikin kamfanin da ake zargi da wawurar dukiyar Jama’a akwai Kamfanin Bamaina Holdings da kuma Speeds International Ltd. Ana zargin Sule da amfani da wadannan kamfanoni wajen satar wasu kudi har Naira Biliyan 1.35

Kafin nan dai manyan Alkalai 2 na babban Kotun Tarayya watau Mai shari’a Adeniyi Ademola da Babatunde Quadri sun fara binciken zargin. Babban Lauyan Hukumar EFCC Chile Okoroma ya nemi Kotu ta sa rana domin a fara shari’a kurum.

Shi dai Lauya Joe Agi wanda shi ne ke kare wadanda ake zargi ya bayyanawa Kotu cewa tuni an taba bada belin wadanda duk ake tuhuma, kuma ba su sabawa sharudan da aka gindaya masu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel