Wata sabuwa: An kashe mutane, an kone gidaje sabon rikicin da ya barke a Adamawa
Rahotanni daga jihar Adamawa sun tabbatar da cewar an kashe mutane da dama tare da raunata wasu ma su yawa a sabon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin jama'ar garin Lafiya da na Boshikiri da ke karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewar rikicin ya barke ne bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe wasu 'yan bijlanti uku yayin da su ka kaiwa wani manomi agaji a gonar sa, lamarin da ya jawo mayar da martani daga jama'ar gari.
Rikicin ya dauki sabon salo a yau, Laraba, bayan an fara kona wuraren ibadar Kiristoci da Musulmi.
Wasu shaidu sun bayyana cewar sun ji karar harbin bindigu, lamarin da ya sa jama'a gudu domin neman mafaka.

Asali: Facebook
Kazalika, kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Adamawa, Abubakar Othman, ya tabbatarwa da gidn talabijin na Channels barkewar rikicin.
Sai dai ya bayyan cewar hukumar 'yan sanda ba ta samu rahoton cewar an rasa rayuka sakamakon rikicin ba tare da sanar da cewar an garzaya da wadanda su ka samu raunuka zuwa asibiti.
Othman ya kara da cewa an kone gidaje, yayin da mutane hudu su ka bace, ba a gan su ba.
DUBA WANNAN: An dasa sojoji a ma'ajiyar motocin Saraki da Dogara a majalisa, hoto
"Abun takaici ne matuka," a cewar sa. "Wadannan kananan hukumomi 2; Lamurde da Guyuk, sun dade su na zaune lafiya.
"Rikicin ya samo asali ne bayan wasu mutane biyu 'yan yankin Lamurde sun afi gona amma sai ba su dawo ba. Bayan kwana biyu sai aka gano gawar daya daga cikinsu a yankin Guyuk. Hakan ya saka mutanen garinsu kai harin daukar fansa bisa zargin cewar an kashe ma su mutane," a cewar Othman.
Bayan ya bayyana cewar jami'an tsaro sun shawo kan lamarin, ya yi kira ga al'ummar yankunan biyu da mayar da takobinsu, su zauna lafiya da juna.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng