Wani Sanata daga babbar jahar PDP ya yi wankan tsarki ya fada jam’iyyar APC

Wani Sanata daga babbar jahar PDP ya yi wankan tsarki ya fada jam’iyyar APC

Wani Sanatan jam’iyyar PDP dake jahar Ribas, Osinakachukwu Ideozu ya sauka yayi wankan tsarki irin na siyasa a ranar Laraba 24 ga watan Oktoba ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Ahmad lawan ne ya sanar da sauyin shekar Sanata Osinakachuku a yayin zaman majalisar dattawan Najeriya na ranar Laraba.

KU KARANTA: Masu yi don Allah: Ta sadaukar da filinta don gina Masallaci, ta bada gudunmuwar dubu 800

Bayan ya bayyana ma takwarorinsa na majalisa sauyin shekar Sanata, sai Ahmad Lawan ya kawo kudirin bukatar majalisar ta dage zamanta na tsawon sati biyu, sa’annan ya taya abokinsa murnar shigowa jam’iyya mai rinjaye a majalisar.

Wani Sanata daga babbar jahar PDP ya yi wankan tsarki ya fada jam’iyyar APC
Sanata Osinachukwu
Asali: Facebook

Wannan sauyin sheka na Sanata Osinkachukwu ya nuna cewa dukkanin Sanatocin da suka fito daga jahar Ribas sun koma jam’iyyar APC, Inda Sanata Andrew Uchendu ya fara komawa APC, yayin da Sanata Magnus Abe aka kafa APC da shi.

A wani labarin kuma, Majalisar dattawa ta kammala aiki akan sabuwar kundin dokokin zaben da take fata shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rattafa hannunsa akansu don hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta aiwatar dasu.

Daga cikin muhimman tanade tanade na kwaskwararren kundin dokokin zaben akwai;

Na’urar tantance masu kada kuri’a da tace a duk inda na’urar tantance masu kara kuri’a ya samu mastala a akwatin zabe, kuma ba’a samu wani na’ura ba har bayan awanni uku, ba za’ayi zaben ba, sai dai a daga shi a sanya lokacin yin sa a cikin awanni 24.

Haka zalika dokar tace ranar zaben fidda gwani na jam’iyyu ba zai wuce kwanaki 150 kafin ranar babban zabe ba, ko yayi kasa da kwanaki 90 kafin ranar zaben. Daga karshe kuma ta sanya adadin kudaden da doka ta amince kowanne dan takara zai iya kashewa a yayin yakin neman zabe; Shugaban kasa naira biliyan 5, Gwamna naira biliyan 1, Sanata naira miliyan 250, da Dan majalisar tarayya naira miliyan 150.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng