Bazan sanya hannu kan duk wani daftari da ban fahimta ba - shugaba Buhari

Bazan sanya hannu kan duk wani daftari da ban fahimta ba - shugaba Buhari

- Akwai lauje cikin nadi a wasu yarjeniyoyin - Buhari

- Sai mun duba mun tantace zamu rattaba hannu

- Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa kadan-kadan

Bazan sanya hannu kan duk wani daftari da ban fahimta ba - shugaba Buhari
Bazan sanya hannu kan duk wani daftari da ban fahimta ba - shugaba Buhari
Asali: Facebook

A kokarin da gwamnatocin Afirka keyi na shiga yarjejeniya da juna, kan tsarin tafiya bai daya a harkar kasuwanci, wanda zai share iyakokin kasashen, kowa ya iya saye da sayarwa a kowacce kasa, shugaba Buhari yace da sake.

A cewar shugaban, a wurin taron, yace sam Najeriya ba zata sake shiga irin wadannan yarjeniyoyi ba sai ta duba ta karanta ta fahimci dukkan ababen da irin wannan yarjejeniya zata haifar, a maimakon yadda ake yi da.

DUBA WANNAN: Siysar Yanki: Abubuwan da Kwankwaso zai iya koya daga Tinubu

Shi dai kasuwanci kan iyakoki da kasuwanni, kan iya takure kasuwannin cikin gida, ya kuma kashe masana'antu daga sayar da nasu hajar, musamman ga irin yadda kasar nan ke son farfado da sabgar noma da industry.

A yanzu shugaba Buhari ya nada Ministan Kasuwanci, Mista Dr Okechukwu Enelamah, da Abba Kyari, babban hadiminsa, kan kwamitin da zasu bi kadin yadda irin wadannan yarjeniyoyi zasu kasance.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng