An kama wani mai gadin Coci dauke da kayan Sojoji guda 6 a Kaduna

An kama wani mai gadin Coci dauke da kayan Sojoji guda 6 a Kaduna

An kama wani mutumi mai suna Mista James, wanda yake gadin Cocin Apostolika dake layin Argungu road a cikin garin Kaduna, sanye da kayan Sojoji, tare da wasu sabbin kayan na Sojoji guda 6 a boye a dakinsa dake Jos road.

Jami’an rundunar tsaro ta farin kaya, Civil defence na suka kama James a yayin da suke tare motoci suna cajesu a akan titin Jos road dake cikin garin Kaduna, kamar yadda kwamandan NSCDC, Modu Bunu ya bayyana.

KU KARANTA: Yan majalisa sun kamala aiki akan sabon kudin dokokin zabe, duba muhimman dokoki 5 daga cikinsu

Sai dai kwamanda Bunu yace ya bayyana cewa James ya shaida musu cewa yana aiki da wani kamfanin tsaro ne, kuma a lokacin da suka kama shi yana kan hanyarsa ta zuwa unguwar Kakuri ne.

An kama wani mai gadin Coci dauke da kayan Sojoji guda 6 a Kaduna
Sojan gona
Asali: Facebook

“Da muka bincika jakarsa, mun gano kayan Sojoji, takalmin, hulan Sojoji, tambarin Yansanda da igiyar daure wango watau belt guda biyu, sa’annan bayan mun rakashi dakinsa dake titin Jos,mun sake kama kayan Sojoji guda Uku.

“Hulunan Sojoji guda uku, rigan sanyi na Sojoji, kananan riguna na Sojoji biyu da sauran kayayyakin da Sojoji ne kadai ya halasta su yi amfani dasu.” Inji Kwamanda Bunu.

Daga karshe Kwamandan yayi kira ga iyaye da u kula da yaransu, tare da jan kunnensu game da bin doka da ka’ida, sa’annan ya ja hankalin shuwagabannin gargajiya dasu tsawata ma jama’ansu game da karya doka da oda.

An kama wani mai gadin Coci dauke da kayan Sojoji guda 6 a Kaduna
Cocin
Asali: Facebook

Sa’annan ya gargadi al’ummar dake unguwannin da suke karkashin dokan ta baci na awanni 24 dasu baiwa jami’an tsaro goyon baya su yi zamansu a gidajensu, don kuwa duk wanda aka kama zai fuskanci tsatstsauran hukunci.

Daga karshe ya bada tabbacin kokarin jami’an tsaro na ganin sun tabbatar da zaman lafiya tare da barazanar tsaro a jahar Kaduna gaba daya.

Ku biyo mu dan samun cikakken rahoton.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel