Kamfanin Jirgin Sama na Najeria zai tabbata nan ba da jimawa ba - Hadi Sirika

Kamfanin Jirgin Sama na Najeria zai tabbata nan ba da jimawa ba - Hadi Sirika

Mun samu cewa karamin Ministan jiragen sama na Najeriya, Sanata Hadi Sirika, ya bayar da tabbacin sa na yau ne ko gobe dangane da kaddamar da Kamfanin Jirgin Sama na Najeria na Nigeria Air da zai fara aiki gadan-gadan a kasar nan.

Baya ga kaddamar da kamfanin jirgin saman a watan Yulin da ya gabata da ake sa ran fara aikace-aikacen sa na jigila a ranar 24 ga watan Dasumba, Ministan ya bayyana rashin yiwuwar hakan inda ya kyautata zato gami da sa ran tabbatuwar hakan nan ba da jimawa ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Jakadan kasar UAE (United Arab Emirates), Fahad Al Taffaq da ya kai ziyara ofishin sa, ya bayyana cewa na ba da jimawa ba wannan gagarumin aiki zai tabbatar a kasar nan.

Kamfanin Jirgin Sama na Najeria zai tabbata nan ba da jimawa ba - Hadi Sirika
Kamfanin Jirgin Sama na Najeria zai tabbata nan ba da jimawa ba - Hadi Sirika
Asali: Twitter

A cewar Sanata Sirika, akwai dankon zumunta dake tsakanin kasar Najeriya da kuma UAE da a halin yanzu ya ke sa ran wannan sabon Jakada zai jajirce wajen habakarta musamman a fannin alaka ta harkokin jiragen sama.

KARANTA KUMA: Irin barnar da aka yi a baya shi ya fi ba ni mamaki da mu ka karbi mulkin Kasar nan - Osinbajo

A na sa bangaren, Ambasada Al Taffaq ya kuma sha alwashin habaka dankon zumunta musamman ta tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu. Ya kuma bayyana shirye-shiryen kasar nan na bude sabon ofishin bayar da Visa a jihar Legas.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewa akwai adadin rayukan Mutane biyar da suka salwanta yayin tashin-tashinar da ta auku cikin jiharsa a ranar Lahadin da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel