Babban dalilin da yasa ba mu kaunar Shugaba Buhari - Gwamnan Benue, Ortom

Babban dalilin da yasa ba mu kaunar Shugaba Buhari - Gwamnan Benue, Ortom

Gwamnan jihar Benue dake a shiyyar Arewa ta tsakiya, Samuel Ortom ya bayyana babban dalilin da ya sa shi da jama'ar jihar sa mafi yawa daga cikin su ba su kaunar shugaban kasa, Muhammadu Buhari kuma basu son ya zarce a 2019.

Gwamnan wanda ya ce ko kusa ba wai don shugaban kasar yana dan kabilar fulani bane, domin a cewar sa, 'yan jihar tasa suna zaune lafiya da duk fulanin dake zagaye da su shekaru aru-aru da suka gabata.

Babban dalilin da yasa ba mu kaunar Shugaba Buhari - Gwamnan Benue, Ortom

Babban dalilin da yasa ba mu kaunar Shugaba Buhari - Gwamnan Benue, Ortom
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta sako tubabbun 'yan Boko Haram 254

Legit.ng Hausa ta samu cewa gwamnan ya ce al'ummar jihar basu son shugaban kasar ne saboda gwamnatin tarayya a karkashin sa ba maida su saniyar ware musamman ma a game da ayyukan raya kasa.

Gwamnan dai yayi wannan kalaman ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman a kan harkokin yada labarai Mista Tahav Agerzua dauke da sa hannun sa a madadain gwamnan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnan na jihar Benue a lashe zaben sa ne a jam'iyyar APC kafin daga bisani ya sauya sheka zawa PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel