Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

- Wata matar aure, Sa'adatu Musa a jihar Nasarawa ta kai karar mijinta kotu saboda baya iya bata hakkinta na kwanciyar aure

- Matar ta yi ikirarin cewar mijin yana kwaracewa shimfidar ta har ta kai ga sau daya ya ke kusantar ta cikin watanni hudu

- Sa'adatu ta roki kotu ta raba aurensu da mijinta, Dembe domin ta ce ba za ta iya zama da mijin da ba zai iya biya mata bukatunta na kwanciyar aure ba

Wata matan aure mai suna Sa'adatu Musa ta shigar da kara Kotun Mararaba da ke Jihar Nasarawa inda ta bukaci a raba aurenta da mijinta, Dembe saboda kaurace wa shimfidar ta da ya ke yi.

Wata mace ta yi karar mijinta a kotu saboda yana kaurace mata a shimfida
Wata mace ta yi karar mijinta a kotu saboda yana kaurace mata a shimfida
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Girma ya fadi: Ana zargin wani maigadi dan shekaru 55 da yiwa 'yar shekaru 10 fyade

Sa'adatu ta yi korafin cewa mijinta baya bata hakkinta na kwanciyar aure inda ta ce sau daya kawai ya kwanta da ita cikin watanni hudu.

Ta ce saboda irin wannan halin na ko in kula da mijinta ke nuna wa game da hakkinta na aure, kwata-kwata ba ta samun gamsuwa da natsuwa cikin auren.

Sa'adata ta fadawa kotu cewar da auri Dembe ne a shekarar 2015 amma har zuwa yau ba su samu bai basu haihuwa ba.

Ta roki kotu da raba aurensu inda ta kara da cewar babu wani sauran soyaya tsakaninsu. Ta ce babu yadda za su cigaba da zaman aure tare tunda baya iya biya mata hakkinta na kwanciyar aure.

Sai dai mijinta, Dembe ya musanta dukkan wannan zargin ta da ke masa.

Alkalin kotun, Mr Ibrahim Shekarau ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba domin bawa ma'auratan damar yin sulhu a tsakaninsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164