Kalli hotunan yadda sabon jakadan UAE a Najeriya ya mikawa Buhari takardar kama aiki cikin salo
Sabon jakandan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Fahad Obaid Al Taffag ya mika wasikar fara aiki a matsayin Ambassada a Najeriya ga Shugaba Muhammadu Buhari yayin wata fareti da aka shirya domin tarbarsa a Fadar Aso Rock da ke Abuja.
Jaridar Legit.ng ta samu wannan rahoto ne daga shafin sada ra’ayi da zumunta na Twitter mallakin ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya @UAEEmbassyNGR.
An yiwa Al Taffag kayatacen faretin soji kana daga baya a mikawa shugaba Muhammadu Buhari takardun sheda da kama aiki.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Facebook

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe
A wani rahoton Legit.ng ta kawo muku cewar gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya gana da shugabanin hukumomin tsaro a jiharsa domin yin bita kan matakan da za a dauka game da rikicin da ya barke a jihar a ranar Alhamis wadda ya yi sanadiyar rasu rayyuka da dukiyoyi a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng