El-Rufai ya ziyarci wuraren da rikicin Kasuwar Magani ya shafa (Hotuna)
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya zaga wasu sassan jihar domin duba irin barnar da ya faru sakamakon rikici da ya barke a jihar bayan wasu matasa sun kaure da fada a Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kujama ta Jihar.
Gwamnan ya tafi ziyaran ne bayan an kafa dokar hana fita a dukkan sassan jihar domin kwantar da tarzoman tare da tabbatar da cewa babu wanda ya samu damar asasa fitinar.
Hukumar 'yan ta reshen jihar Kaduna ta sanar da cewar ta damke wasu matasa 22 da ake zargin suna da hannu cikin ingiza rikicin kuma ana cigaba da zurfafa bincike kafin daga bisani a gurfanar da su gaban kotu.
El-Rufai ya kai ziyarar ne tare da mai bashi shawara kan harkokin siyasa kuma zababen dan takarar kujerar Sanata a jam'iyyar APC na mazabar Kaduna ta Tsakiya, Malam Uba Sani.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: 2019: Matasan kudancin Kaduna sun ci alwashin kayar da El-Rufa'i zabe

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Kawo yanzu, a kalla mutane 65 ne aka ruwaito cewar sun rasa rayyukansu sakamakon barkewar rikicin.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Gwamnan ya yi kira da al'ummar jihar su zauna lafiya da zuna, ya kuma ci alwashin binciko duk wadanda ke da hannu a rikicin tare da mika su gaban hukuma domin a hukunta su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng