Da dumin sa: Wani sanannen babban limami ya rasu a Kaduna

Da dumin sa: Wani sanannen babban limami ya rasu a Kaduna

Wani babban sanannen malamin Islama, kuma limamin masallacin dake kan hanyar Yahaya (watau Yahaya Road) na Juma'a a unguwar Rimi, mai suna Malam Hassan Muhammad ya riga mu gidan gaskiya.

Mun samu cewa dai Malam Hassan ya rasu ne ranar Asabar din da ta gabata bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya a gidan sa dake can garin na Kaduna.

Da dumin sa: Wani sanannen babban limami ya rasu a Kaduna
Da dumin sa: Wani sanannen babban limami ya rasu a Kaduna
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa an kuma yi jana'izar sa a ranar Lahadi a masallacin na Juma'a dake a kan hanyar Yahaya da karfe 1:30 na rana bayan Sallar Azahar.

Muna rokon Allah ya jikan sa ya kuma kyautata tamu idan tazo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel