Labari mai dadi: Farashin wasu nau'ikan abinci 4 ya sauka a watan Satumba - NBS

Labari mai dadi: Farashin wasu nau'ikan abinci 4 ya sauka a watan Satumba - NBS

- NBS ta bayyana cewar farashin wasu kayan abinci ya sauka a watan Augusta

- Kayayakin abincin da su kayi sauki sun hada da doya, tumatur, shinkafa da kwai

Labari mai dadi: Farashin wasu kayan abinci ya sauka a watan Satumba - NBS
Labari mai dadi: Farashin wasu kayan abinci ya sauka a watan Satumba - NBS
Asali: Facebook

Hukumar Kididiga na Kasa (NBS) ta bayyana cewar farashin wasu kayan abinci ya sauka a kasar cikin watan Satumban 2018.

Daily Nigerian ta ruwaito cewar cibiyar ta bayar da wannan sanarwan ne cikin mujjalar ta mai taken "Selected Food Price Watch" na watan Satumban 2018 da aka fitar a babban birnin tarayya, Abuja.

Labari mai dadi: Farashin wasu kayan abinci ya sauka a watan Satumba - NBS
Labari mai dadi: Farashin wasu kayan abinci ya sauka a watan Satumba - NBS
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Dandalin Kannywood: Abinda ya sa mazaje ke shakkar auren 'yan fim - Kyauta Dillaliya

Ta ce farashin kwan kajin turawa madaidaita guda 12 da ragu daga N472.73 a watan Augusta zuwa N474.13 a watan Satumban 2018.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, kudin kilogram daya na tumatur ya ragu daga N336.65 a cikin watan Augusta zuwa N328.26 a watan Satumba.

Kazalika, rahoton nuna cewar farashin kilogram 1 na doya ya rage daga N292.97 a watan Augusta zuwa N292.97 a watan Satumba a kasuwanni.

Daga karshe farashin shinkafa na kasashen waje ya yi sauki shima daga N375.02 a watan Augusta zuwa N371.32 a watan Satumban shekarar 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164