Kasar Algeria ta haramta sanya Niqabi a wajajen aiki

Kasar Algeria ta haramta sanya Niqabi a wajajen aiki

Gwamnatin kasar Algeria ta haramtawa mata sanya tufafin Musulunci wanda akafi sani da Niqabi a wajajen aiki a jiya Alhamis, 19 ga watan Oktoba, 2018 bisa ga wasu dalilai.

Kasar Larabawan ta kasance cikin rikice-rikicen addini yayinda akidoji da dama sun bayyana a kasar tun bayan yakin basasan kasar a shekaran 1992 lokacin da sojoji suka watsar da sakamakon zabe bayan ya bayyan jam’iyyar Musulmai zata samu nasara.

Yawancin mutanen kasar Algeriya sun kasance suna kokarin kwaikwayon halaye da rayuwan Turawa saboda kusantar kasar da nahiyar Turai, saboda haka, yawancin yan matan garin basu sanya tufafi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kasar Algeria ta haramta sanya Niqabi a wajajen aiki
Kasar Algeria ta haramta sanya Niqabi a wajajen aiki
Asali: Facebook

Wannan labari na zuwa ne yayinda addinin Musulunci ke sake yawaita a kasashen Turai amma kasashen Larabawa na kyamatan addinin da aka haifi iyayensu akai.

A kwanakin baya, majalisar dokokin kasar Australiya ta halaltawa dukkan mace Musulmar da ta sanya Niqabi saboda tabbatar mata da yancin kanta. Wannan abu ya faru ne yayinda wata Sanata Hanson ta nuna kiyayyarta ga Niqabin a zauren Majalisa.

KU KARANTA: Jihohin arewa 4 da ke sahun gaba a kuncin rayuwa

Martani kan hakan, babban lauyan kasar Australiya ya jaddada cewa babu abinda zai sanya su haramtawa Musulmai sanya Niqaabi saboda addininsu ne kuma bai shafi kowa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng