Ba mutunci: Mama Taraba ta kwashe dukkan kayan da ta bawa jam'iyyar APC

Ba mutunci: Mama Taraba ta kwashe dukkan kayan da ta bawa jam'iyyar APC

- Tsohuwar Ministan Harkokin Mata, Aisha Alhassan ta kwashe dukkan kayaykin da ta bawa jam'iyyar APC tallafi a Jalingo

- Kayayakin da Ministan ta kwace sun hada da kwamfuta, kujeru, tebura, na'urar AC wasu kayayakin

- Alhassan ta ce jam'iyyar APC ba ta cancanci ta amfana da kayayakin ta ba duba da irin rashin adalcin da tayi mata

Tsohuwar Ministan Harkokin Mata wadda tayi murabus daga mukaminta bayan ta fice daga jam'iyyar APC, Aisha Alhassan (Mama Taraba) ta kwace kwamfutoci da kujeru da ta bawa ofishin APC da ke Jalingo a matsayin gudunmawarta.

Sakataren yadda labarai na APC a jihar, Mr Aaron Artimas ya ce Mama Taraba ta kuma kwace na'urar sanyaya daki wato AC da tebura da carpet da ta siyawa jam'iyyar kafin ficewar ta.

Ba mutunci: Mama Taraba ta kwashe dukkan kayan da ta bawa jam'iyyar APC

Ba mutunci: Mama Taraba ta kwashe dukkan kayan da ta bawa jam'iyyar APC
Source: Facebook

"Wannan abin ya bamu kunya amma gaskiya ne. Tsohuwar Ministan ta kashe dukkan kayayakin da ta siyawa Ofishin APC a lokacin da ta ke jam'iyyar mu," kamar yadda Artimas ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ranar Laraba a Jalingo.

DUBA WANNAN: Magudin Jarabawa: Gwamnati ta maka dan takarar gwamnan PDP a kotu

Artimas ya ce shugabanin jam'iyyar sun amince da kwashe kayayakin da ta siyawa jam'iyyar inda ya bayyana cewa yayi mamakin yadda tsohuwar Minista za ta nuna karanci na kwace duk wani abinda ta siya wa jam'iyyar a baya.

Da ta ke mayar da martani kan batun, Mama Taraba ta bayyana cewar ba ita ta bayar da umurin a kwace kayayakin ba amma ta goyi bayan wadanda suka kwashe kayayakin saboda irin rashin adalcin da APC tayi mata.

"Ni na siya kayayakin da kudi na, lokacin da masu yi min hidima suka fada min cewar sun tafi sakatariyar jam'iyyar domin kwashe kayayakin, na basu izinin yin hakan domin APC ba ta cancanci in bata wani kyauta ba saboda rashin adalcin da ta min," Inji Mama Taraba a hirar da tayi da NAN daga Abuja.

Source: Legit

Mailfire view pixel