Gwamna Fayemi ya nada wasu muhimman mukamai da zasu tafiyar da gwamnatinsa

Gwamna Fayemi ya nada wasu muhimman mukamai da zasu tafiyar da gwamnatinsa

Sabon gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi ya sanar da nadin wasu muhimman mukamai a gwamnatinsa jim kadan bayan kamala bikin rantsar da shi daya gudana a ranar Talata 16 ga watan Oktoba, kamar yadda rahoton jaridar Punch ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya sanar da sunan Mista Abiodun Oyebanji a matsayin sabon sakataren gwamnatin jahar Ekiti, Mista Biodun Omeyele a matsayin shugaban ma’aikacin fadar gwamnatin jahar, da kuma Yinka Oyebode a matsayin sakataren watsa labaru.

KU KARANTA: Kaakakin wani gwamna ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Gwamna Fayemi ya nada wasu muhumman mukamai da zasu tafiyar da gwamnatinsa
Gwamna Fayemi
Source: Depositphotos

Abiodun Oyebanji tsohon malamin jami’a ne, kuma ya taba rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Eikti a zamanin mulkin Gwamna Otunba Niyi Adebayo, haka zalika shine kwamishinan kasafin kudi da tsara tsare tsaren tattalin arziki a zamanin mulkin Fayemi na farko.

Shi kuwa Omoyele, ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Ijero, sa’anann ya taba zama mataimaki na musamman a ofishin gwamnan jahar Ekiti, yayin da sabon sakataren watsa labaru Oyebode ya kasance gogaggen dan jarida, kuma Kaakakin gwamna Fayemi a wa’adinsana farko.

Haka zalika Oyebode ya cigaba da aiki tare da Fayemi har lokacin da ya zama ministan albarkatun kasa a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, daga karshe sanawar ta kara da cewa nadin ya fara aiki ne nan take.

A jiya Talata ne aka rantsar da Fayemi a matsayin sabon gwamnan jahar Ekiti inda ya amshi mulki daga hannun tsohon gwamnan Ayodele Fayose, sai dai gwamnann ya koka, inda yace a tsohuwar gwamnatin ta kara adadin bashin da ake bin jahar zuwa naira biliyan 170.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Legit

Online view pixel