Takarar Sanata: Makarfi ya kunyata jam'iyyar PDP, ya ce akai kasuwa

Takarar Sanata: Makarfi ya kunyata jam'iyyar PDP, ya ce akai kasuwa

- Makarfi ya kunyata jam'iyyar PDP, ya ce akai kasuwa

- Yace shi bai da ra'ayin yin takarar Sanata

Daya daga cikin wadanda suka yi takarar tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya karyata rade-raden cewa an bashi tikitin takarar Sanata a jam'iyyar a zaben 2019 biyo bayan rashin nasarar da yayi a zaben fitar da gwani.

Takarar Sanata: Makarfi ya kunyata jam'iyyar PDP, ya ce akai kasuwa
Takarar Sanata: Makarfi ya kunyata jam'iyyar PDP, ya ce akai kasuwa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bafarawa na shirin barin PDP ne?

Shi dai Makarfi ya yi takarar tikitin shugaban kasa ne tare da wasu mutane 11 a jam'iyyar ta PDP amma bai samu nasara ba inda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.

To sai dai wasu rahotannin da sukayi ta yawo sune na cewa jam'iyyar ta PDP ta baiwa dukkan wanda yayi takarar shugaban kasar amma bai samu nasara ba tikitin takarar Sanata kai tsaye tun kafin zaben.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ekiti dake a yankin Kudu maso yammacin kasar nan mai barin gado, Ayodele Fayose ya tattara yanasa-yanasa ya fice daga jihar biyo bayan hannun ta takardun barin gwamnati da yayi a ranar Juma'ar da ta gabata.

Gwamnan dai ya bar jihar ne da yammacin ranar Lahadi jim kadan bayan kammala wata ibada ta musamman da yayi a cocin gidan gwamnatin jihar wadda ta samu halartar manya a ciki da wajen jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng