Har yanzu ban farfado daga rigimar zaben Abiola ba – tsohon Shugaban APC Oyegun

Har yanzu ban farfado daga rigimar zaben Abiola ba – tsohon Shugaban APC Oyegun

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa baki daya John Odigie Oyegun yayi hira da Jaridar Daily Trust inda ya tattauna a kan batutuwa na siyasar Najeriya da lokacin sa a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC.

Har yanzu ban farfado daga rigimar zaben Abiola ba – tsohon Shugaban APC Oyegun

Oyegun yana nemawa Buhari goyon baya a zaben 2019
Source: UGC

A kwanakin baya ne aka cire John Odigie Oyegun, aka nada Adams Oshiomhole a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki. Oyegun ya bayyana cewa yayi alfahari da abin da APC ta zama inda ya kuma nemi a sake zaben Shugaba Buhari.

John Oyegun ya nuna cewa bai farfado daga abin da ya fari a lokacin zaben Marigayi MKO Abiola ba inda kasuwancin sa ya rushe. Oyegun yace sai da aka shiga kamfanin sa da ke Benin sau 3 saboda kurum su na adawa da mulkin Soja.

KU KARANTA: Irin ayyukan da nayi a ofis za su sa mutane su sake zabe na – Buhari

A wancan lokaci dai Cif John Oyegun su ne ke sahun gaba wajen yakar Gwamnatin Babangida a lokacin zaben 12 ga Watan Yuni wanda Abiola yayi nasara. A karshe dai yace kusan sun ci ma burin su duk da MKO Abiola ya rasu a daure.

Shugaban na APC daga 2014 har 2018 ya nuna cewa har gobe yana tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Oyegun yace Najeriya ta na bukatar mutum ne mai rikon amana da tambarin gaskiya kamar yadda aka yi sa’ar Buhari a yanzu.

John Oyegun ya nemi jama’a su marawa Shugaba Buhari wanda yake fada da rashin gaskiya baya. Oyegun ya kara da cewa ba gaskiya bane ace Gwamnatin nan tana fada ne da ‘Yan adawa kurum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel