Na cancanci ‘Yan Najeriya su sake zabe na a 2019 inji Shugaba Buhari

Na cancanci ‘Yan Najeriya su sake zabe na a 2019 inji Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan Najeriya cewa ya dace ya zarce a kan mulki

- Shugaban kasar yace ayyukan da yayi za su sa jama’a su sake zaben sa a 2019

- Muhammadu Buhari ya nemi mutane su mara masa baya ya zarce kan kujera

Na cancanci ‘Yan Najeriya su sake zabe na a 2019 inji Shugaba Buhari

Buhari yayi kira ga mutane su sake zaben sa domin ya gyara Najeriya
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi mutanen Najeriya su sake zaben sa a wani karon a 2019 domin ya cigaba da irin kokarin da yake yi na gyara kasar nan. Shugaba Buhari yayi wannan kira ne kwanan nan.

Premium Times ta rahoto Shugaban kasar yana wannan roko ne a Garin Abuja lokacin da ya gana da manyan Malaman addini. Shugaban kasar yace yana alfaharin yadda abubuwa su ka canza a kasar bayan hawan sa kan mulki.

KU KARANTA: Obasanjo ya fara yiwa Atiku kamfen a wata kasar waje

Shugaba Buhari yace an wuce lokacin satar dukiyar al’umma da kuma rashin amana a Najeriya. A don haka ne Shugaban kasar yake ganin ya ci a ce mutane sun sake mara masa baya a zaben da za ayi a 2019 domin ya zarce a kujera.

Shugaba Buhari ya nemi Malaman na addini su dage wajen ganin al’umma ta hada kai inda ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta kawo karshen duk wani rikici da ake yi a Kasar tare da ganin an wanzar da zaman lafiya.

Har wa yau, Shugaban na Najeriya yayi alkakwari za ayi zaben kirki na adalci da gaskiya a 2019 inda ya nemi wadanda su ka sha kashi a zabukan fitar da gwani su tafi Kotu ko kuma su nemi maslaha a Jam’iyya cikin kwanciyar hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel