Dakarun sojin Najeriya sun yiwa 'Yan ta'adda na Boko Haram Ruwan Wuta a jihar Borno

Dakarun sojin Najeriya sun yiwa 'Yan ta'adda na Boko Haram Ruwan Wuta a jihar Borno

Mun samu cewa a ranar Juma'ar da ta gabata ne dakarun sojin kasa na Najeriya masu atisaye na Operation Lafiya Dole, suka samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan ta'adda na Boko haram a kauyen Arege dake jihar Borno.

Ko shakka ba bu rayukan 'yan ta'adda da dama sun salwanta yayin wannan dauki ba dadi da dakarun soji inda wasu suka yi jarumtar tserewa da munanan raunuka na harsashin bindiga.

Dakarun sojin Najeriya sun yiwa 'Yan ta'adda na Boko Haram Ruwan Wuta a jihar Borno

Dakarun sojin Najeriya sun yiwa 'Yan ta'adda na Boko Haram Ruwan Wuta a jihar Borno
Source: Facebook

Rahotan kamar yadda kakakin hukumar sojin kasa ya ruwaito, Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana cewa, a yayin wannan artabu dakarun sojin sun kuma samu nasarar kwato wata Mota guda da kuma wasu Motocin yaki uku daga hannun 'yan ta'addan.

KARANTA KUMA: Allah ne ya zabi Atiku domin ceto Najeriya daga Buhari - Osuntokun

Sai dai kamar yadda Hausawa kan ce sai an sha wuya akan sha dadi akwai dakarun soji 6 da suka jikkata yayin wannan bakin gumurzu da 'yan ta'adda da a halin yanzu ke samun kulawa a asibiti dakarun soji dake birnin Maiduguri.

Kakakin ya kuma tunatar da al'ummar kasar nan akan su ci gaba kwazon shigar da korafin duk wani motsi na rashin yarda da ba su aminta da shi ba zuwa ga hukumomin tsaro da suka dace domin kawar ma su da fargaba da rashin samun sukuni a zuciya.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel