'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum guda a harin da aka kaiwa tawagar gwamna Tambuwal

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum guda a harin da aka kaiwa tawagar gwamna Tambuwal

- Wani matashi ya rasa ransa bayan magoya bayan APC da PDP sun yi arangama a Sokoto

- Matashi, Imrana Ahmad Alkanchi, ya mutu ne bayan harsashin bindiga ya same shi

- Lamarin ya faru ne bayan wasu da ake zargin magoya bayan APC ne sun yi yunkurin hana gwamna Tambuwal da tawagar sa wucewa ta unguwar su

A kalla mutum daya ne ya rasa ransa bayan magoya bayan manyan jam'iyyun Najeriya biyu; APC da PDP, sun yi arangama a garin Sokoto, a jiya Asabar, 13 ga watan Oktoba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar wani matashi, Imrana Ahmad Alkanchi, mai shekaru 22 ya mutu bayan harsashin bindiga ya same shi yayin hargitsin.

Zayyanu wani dan uwa ga marigayi Imrana ne ya tabbatar da mutuwar da mutuwar matashin.

'Yan daba sun tare hanyar gwamna Tambuwal a Sokoto, mutum daya ya mutu

Tambuwal da Wamako
Source: Twitter

A cewar Zayyanu, ma'aikacin sashen adana bayanai a jami'ar Sokoto, harsashin bindiga ya samu Imrana ne yayin da yake jiran babur bayan ya dawo daga kasuwar Gawon Nama.

A cewar rahoton Daily Trust, an samu hargitsi ne yayin da wasu 'yan daba da ake zargin magoya bayan jam'iyyar APC ne sun yi yunkurin hana gwamna Tambuwal wucewa ta yankinsu. Lamarin da ya sa magoya bayan gwamnan mayar da martani.

A unguwar Gawon Nama ne gidan jagoran jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Aliyu Wamako, ya ke.

DUBA WANNAN: Yarjejeniyar da Saraki ya cimma da Sanatocin APC a kan batun tsige shi

Jama'a da dama ne su ka yi dandazo a filin tashi da saukar jirage na Sultan Abubakar II domin tarbar Tambuwal a yayin da ya ke dawowa jihar Sokoto a karo na farko tun bayan kammala zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP da aka yi a Fatakwal.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto, DSP Cordelia Nwewe, ya ce har yanzu su na gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel