Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya soma wata muhimmiyar ganawa da 'yan majalisar tarayya na APC

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya soma wata muhimmiyar ganawa da 'yan majalisar tarayya na APC

Labarin da muke samu yanzu da dumin sa shine na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yanzu haka yana cikin wata muhimmiyar ganawa ta sirri da mambobin majalisar tarayya 'ya'yan jam'iyyar APC a fadar sa dake a Villa, Abuja babban birnin tarayya.

Mun samu cewa taron wanda yanzu haka yake gudana a bayan labule ana yin sa ne a dakin taro na banquet Hall kuma ya samu halartar ya'yan jam'iyyar ta APC da dama.

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya soma wata muhimmiyar ganawa da 'yan majalisar tarayya na APC

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya soma wata muhimmiyar ganawa da 'yan majalisar tarayya na APC
Source: Facebook

KU KARANTA: Bafarawa na shirin komawa APC

Kawo yanzu dai ba'a san abun za'a tattauna ba a cikin taron amma dai ana zaton cewa ganawar ba zata rasa nasaba da sake bude majalisar ba bayan dogon hutun da suka dauka da kuma dambarwar siyasar da ke a can.

Cikakken rahoto kan taron na nan tafe.

A wani labarin kuma, Haddiyyar kungiyar dake rajin kare hakkin 'yan kabilar yarbawa a Najeriya watau Afenifere ta yi tsokaci game da zabar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi a matsayin mataimaki da Atiku Abubakar yayi.

Mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere, Yinka Odumakin shine yayi wannan tsokacin a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin kungiyar inda yace yanzu ya zama dole ga 'yan takarar su fito da tsarin su na yadda za su sauya fasalin kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel