Duniya: Abokai da hadiman Fayose sun ki amsa gayyatar sa ta bankwana

Duniya: Abokai da hadiman Fayose sun ki amsa gayyatar sa ta bankwana

Abokan arziki da hadiman gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele Fayose sun kunyatta shi sakamakon kin hallartan wallimar cin abinci da ya shirya a daren Juma'a domin bankwana da su.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito misalin karfe 11 na dare, mutane kasa da 20 ne kawai suka iso wajen walimar da ya kamata a fara tun karfe 7 na yamma.

Kuma cikin mutane 20 din galibinsu masu gadi ne da ma'aikata gidan gwamnatin da kuma masu kade-kade da raye-raye da aka gayyata.

Duniya: Abokai da hadiman Fayose sun ki amsa gayyatar sa ta bankwana

Duniya: Abokai da hadiman Fayose sun ki amsa gayyatar sa ta bankwana
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2019: 'Yan takarar shugaban kasa 15 na bazata

Rashin hallartar bakin da aka gayyata ya saka anyi asarar abinci da aka tanada dominsu.

Wata majiya daga gidan gwamnatin ta shaida wa NAN cewar wanda aka gayyata sun ki amsa gayyatar ne saboda basu ji dadin wasu abubuwa da gwamnan ya aikata ba kafin ya mika mulki.

Wata majiyar da ta nemi a sakayya sunanta ta ce gwamnan ya biya kansa da mataimakinsa kudade masu tsoka a matsayin kudin barin aiki tare da motocci amma bai bawa mukarrabansa ko taro ba.

A yayin da ya ke tsokaci kan lamarin, wani ma'aikaci a gidan gwamnatin ya ce bai yi mamakin abinda ya faru ba domin haka dama halin mutane ya ke. Sukan kusance ka ne kawai lokacin da kake da kudi ko mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel