Hadaddiyar kungiyar Yarbawa ta yi magana game da takarar Atiku da mataimakin sa Obi

Hadaddiyar kungiyar Yarbawa ta yi magana game da takarar Atiku da mataimakin sa Obi

- Hadaddiyar kungiyar Yarbawa ta yi magana game da takarar Atiku da mataimakin sa Obi

- Sun ce yanzu ya kamata su fara shirin sake fasalin kasa

- Mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere, Yinka Odumakin ne yace haka

Haddiyyar kungiyar dake rajin kare hakkin 'yan kabilar yarbawa a Najeriya watau Afenifere ta yi tsokaci game da zabar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi a matsayin mataimaki da Atiku Abubakar yayi.

Hadaddiyar kungiyar Yarbawa ta yi magana game da takarar Atiku da mataimakin sa Obi

Hadaddiyar kungiyar Yarbawa ta yi magana game da takarar Atiku da mataimakin sa Obi
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An kama barawo sanye da kayan sojoji a Najeriya

Mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere, Yinka Odumakin shine yayi wannan tsokacin a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin kungiyar inda yace yanzu ya zama dole ga 'yan takarar su fito da tsarin su na yadda za su sauya fasalin kasar nan.

Idan dai ba a manta ba, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zabi tsohon gwamnan na Anambra Peter Obi a matsayin mataimaki bayan wata ganawar sirri da sukayi a jiya.

A wani labarin kuma, Bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya ya yafewa Atiku Abubakar tare da goya masa baya a kan takarar da yake yi ta shugaban kasa a 2019, wasu manyan janar-janar har biyu suma sun nuna goyon bayan su gareshi.

Manyan tsaffin jami'an sojin dai su ne Manjo Janar David Jemibewon da kuma Birgediya Janar Ajibola Togun wadanda kuma dukkan su sun rike manyan mukamai a lokutan baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel