Zaben 2019: Guguwar Atiku na cigaba da mamaya a tsakanin kushoshin kasar nan

Zaben 2019: Guguwar Atiku na cigaba da mamaya a tsakanin kushoshin kasar nan

- Guguwar Atiku na cigaba da mamaya a tsakanin kushoshin kasar nan

- Takarar ta shi ta samu goyon bayan Janar-janar 2

- Sun ce suna da yakinin ya fi Shugaba Buhari

Bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya ya yafewa Atiku Abubakar tare da goya masa baya a kan takarar da yake yi ta shugaban kasa a 2019, wasu manyan janar-janar har biyu suma sun nuna goyon bayan su gareshi.

Zaben 2019: Guguwar Atiku na cigaba da mamaya a tsakanin kushoshin kasar nan

Zaben 2019: Guguwar Atiku na cigaba da mamaya a tsakanin kushoshin kasar nan
Source: Twitter

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta nada sabon kakakin ta

Manyan tsaffin jami'an sojin dai su ne Manjo Janar David Jemibewon da kuma Birgediya Janar Ajibola Togun wadanda kuma dukkan su sun rike manyan mukamai a lokutan baya.

Legit.ng dai ta samu cewa da suke tsokaci game da takarar ta Atiku, sun bayyna a lokutan daban-daban cewa tabbas Atiku yana iya lashe zaben na 2019 kuma suna da yakinin cewa zai fi Shugaba Buhari tabuka abun kirki idan ya zama shugaban kasa.

A wani labarin kuma, Haddiyyar kungiyar dake rajin kare hakkin 'yan kabilar yarbawa a Najeriya watau Afenifere ta yi tsokaci game da zabar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi a matsayin mataimaki da Atiku Abubakar yayi.

Mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere, Yinka Odumakin shine yayi wannan tsokacin a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin kungiyar inda yace yanzu ya zama dole ga 'yan takarar su fito da tsarin su na yadda za su sauya fasalin kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel