Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja (Hotuna)

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja (Hotuna)

Bisa dukkan alamu dai ta tabbata cewar tsohon dan takarar gwamna a jihar Kano, Mallam Salihu Sagir Takai ne dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Wannan na zuwa ne bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa tsakanin bangaren Sanata Mas'ud El-Jibril Doguwa da ke goyon bayan Takai da kuma bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke son surukinsa Engr. Abba Yusuf ya zama dan takarar.

Legit.ng ta tattaro cewar Takai ya tafi hedkwatan jam'iyyar PDP da ke Abuja inda ya karbo tutan takarar gwamna kamar yadda wani bibiyar shafin Twitter @mubarakbnyunus ya wallafa a shafinsa.

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya zolaye Buhari a kan nadin ministoci

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja
Source: Twitter

Wata majiyar ta kuma ruwaito cewar an bawa Kwankwaso kwanaki biyu domin ya zabo wanda zaiyi takara a matsayin mataimakin gwamna a jihar.

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja
Source: Facebook

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja

Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja
Source: Twitter

A kwanakin baya, Legit.ng ta kawo muku cewar wasu magoya bayan Kwankwaso sun kone katin jam'iyyarsu na PDP saboda kishin-kishin jin cewar dan takarar da Kwankwaso ke so ba zai samu tikitin takarar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel