Kakaba takunkumin hana fita kasashen waje: PDP tayi kumfar baki

Kakaba takunkumin hana fita kasashen waje: PDP tayi kumfar baki

- Jam'iyyar PDP tayi tir da takunkumin hana fita kasashen waje da shugaba Buhari ya kafa wa wasu manyan mutane 50 a Najeriya

- Hakan ya faru ne sakamakon kafa dokar Executive Order 6 da ta baiwa gwamnati damar bincikar duk wani wanda ya mallaki sama da N50 miliyan

- PDP tayi kira da dukkan masu kishin demokradiyya su tashi tsaye domin su yaki dokar

Jam'iyyar adawa ta PDP tayi Allah wadai da takunkumin hana fita kasashen ketare da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kan wasu manyan 'yan Najeriya 50 inda ta ce Najeriya ta kama hanyar kama karya da murdiya.

A dai yau Asabar, 13 ga watan Oktoba ne shugaba Buhari ya bayar da umurnin fara aiki da dokar Executive Order 6 (E06) wadda ta bawa gwamnati damar bincikar duk wani wanda ya mallaki kudi fiye da miliyan 50 tare da sanya idanu kan shige da fice na kudadensu.

PDP ta yi mayar da martani kan takunkumin hana fita kasar waje da Buhari ya saka

PDP ta yi mayar da martani kan takunkumin hana fita kasar waje da Buhari ya saka
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Atiku ya zolaye Buhari a kan nadin ministoci

A hirar da ya yi da Thisday bayan sanarwar kafa dokar, Sakataren Jam'iyyar PDP na kasa, Mr Kola Ologbondiyan ya yi kira da dukkan masu rajin kare demokradiyya da su tashi su yaki wannan takunkumi da shugaban kasan ya saka.

Ologbondiyan ya kara da cewa jam'iyyar PDP za ta bayyana matsayar ta kan dokar a jam'iyyance nan da wani lokaci.

A halin yanzu dai ba'a bayyana sunayen mutane 50 din da dokar za ta hau kansu ba sai dai wasu na ganin shugaban kasar ya saka dokar ne domin ya musgunawa abokan hammayarsa musamman yanzu da ake tunkarar babban zabe.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya sanar, shugaba Buhari ya umurci Attorney-General na kasa da Ministan Shari da su gaggauta fara tabbatar da dokar ba tare da bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel