Soji sun ragargaji 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna

Soji sun ragargaji 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna

- Sojin Najeriya sunyi nasarar kashe wasu 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna

- Sojin sun kai sumamen ne a wata mafakar 'yan bindagan da ke dajin Kamuku a karamar hukumar Birnin Gwari

- Dakarun Sojin sun kuma sake kai wata sumame a Unguwar Maigwari inda suka tartwatsa wata mafakar masu garkuwa da mutane

Dakarun Sojin Najeriya karkashin atisayen Operation Whirl Punch na Division 1 da ke Kaduna sunyi nasarar kashe 'yan dadi bindiga da masu garkuwa da mutane da dama a dajin Kamuku da ke Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Soji sun ragargaji 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna
Soji sun ragargaji 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hanyoyi 6 da ake amfani da goro da ya dace ku sani

Sanarwar da ta fito daga mataimakin Direktan yada labarai na 1 Division Nigerian Army, Colonel Muhammad Dole a jiya ya ce Sojojin sun kai sumame mafakar 'yan daban a ranar 9 ga watan Oktoba inda suka kwato makamai da wasu kayayaki.

Kazalika, ya kuma ce sojin tare da 'yan banga sun sake kai sumame a wani mafakar 'yan bindigan da ke Kidandan inda suka kashe mutum guda sannan sauran suka tsere da raunukan bindiga. Sojin sun kwato AK 47 guda da wasu harsashai.

Bugu da kari, Sojin sun kuma sake yiwa wasu masu garkuwa da mutane dirar mikiya a Unguwar Maigwari a da ke hanyar Doka - Layin Rijana inda suka tarar da kayan maye da muggan kwayoyi da sauransu.

Sojin sun kama dan leken asiri guda daya da kuma bindigogi na farauta guda uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel