Yaki da Kwarapshan: Bayan da kotu ta bashi dama, shugaban Najeriya ya sanya wa manyan kasar nan 50 takunkumi, babu su babu fita kasar waje

Yaki da Kwarapshan: Bayan da kotu ta bashi dama, shugaban Najeriya ya sanya wa manyan kasar nan 50 takunkumi, babu su babu fita kasar waje

- Shugabancin kasa ta haramtawa wasu yan Najeriya fita kasar

- Masu kadarori da kudade sama da miliyan 50 ne

- Duk wasu shige da ficen kudin su ana lura dasu

Yaki da Kwarapshan: Bayan da kotu ta bashi dama, shugaban Najeriya ya sanya wa manyan kasar nan 50 takunkumi, babu su babu fita kasar waje

Yaki da Kwarapshan: Bayan da kotu ta bashi dama, shugaban Najeriya ya sanya wa manyan kasar nan 50 takunkumi, babu su babu fita kasar waje
Source: UGC

Ofishin Shugaban kasa, Muhammad Bukhari ya sanar da haramtawa wasu 'yan Najeriya 50 tafiye tafiye zuwa kasashen ketare.

'Yan Najeriya, da ba a bayyana sunansu ba, sun hada da wadanda kadarorin su suka kai Naira miliyan 50 zuwa sama, abin bincike ne akan rashawa.

Wasu zasu ga kamar wannan na da alaka da siyasa, musamman ganin sai yanzu aka kawo wannan gabsa, ana dab da zabe.

Ba'a dai san ko cikinsu harda Atiku Abubakar ba, dan takarar PDP, ko manyan mukarrabansa irinsu Bukola Saraki wadanda ke shan bincike tun 2015.

Watakil kuma, jama'a suyi mamaki idan ba'a sanya irinsu Bola Tinubu cikin jerin sunayen ba, musamman ganinsuma sun zama manyan hamshaqai a kasar nan, harda jiragen sama.

Yaki da Kwarapshan: Bayan da kotu ta bashi dama, shugaban Najeriya ya sanya wa manyan kasar nan 50 takunkumi, babu su babu fita kasar waje

Yaki da Kwarapshan: Bayan da kotu ta bashi dama, shugaban Najeriya ya sanya wa manyan kasar nan 50 takunkumi, babu su babu fita kasar waje
Source: UGC

Ba'a tsammaninsu Goodluck, IBB, ko Obasanjo zasu sami shiga wannan sabon list, amma komai na iya kasancewa, tunda lokacin gwamnatin yazo dab da qarewa, ko a zarce, ko a fado.

Maganar ta fito ne daga mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu.

Yace wannan matakin tabbatar da dokar zababbe mai lamba 6, wadda shugaban kowacce kasa ke iya sanya wa, "Kowacce kadara mai darajar Naira miliyan 50 ko sama da haka abin bincike ce kuma dole a kare ta daga almubazzaranci har sai an kammala binciken ta."

DUBA WANNAN: Aljannu sun musulunta a hannun Dahiru Bauchi

Mista Shehu, ya kara da cewa duk wani shige da ficen kudin mutanen ana lura dashi ta cibiyoyin da suka kamata.

Biyo bayan tabbatar da dokar, Executive Order 006, Shugaban kasa Muhammad Bukharin, ya wajabtawa Attorney-General na tarayya da ministan shari'a dasu tabbatar da dokar ba tare da bata lokaci ba.

A sakamakon haka ne Nigeria Immigration Services da sauran cibiyoyin tsaro irinsu 'yansanda, na farin kaya, na boye, da na fili, da ma DSS, sun soma zuba ido akan mutane 50 tare da haramta musu barin kasar har sai an wanke su daga zargin rashawa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel