Idan har na zama shugaban kasa: Ba zan dauki watanni 6 kafin bayyana mukarrabaina ba- Atiku

Idan har na zama shugaban kasa: Ba zan dauki watanni 6 kafin bayyana mukarrabaina ba- Atiku

- Atiku Abubakar ya ce idan har aka zabe shi a 2019, to kuwa ba zai dauki tsawon watanni 6 kafin ya bayyana sunayen mukarraban gwamnatinsa ba

- Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a ranar ne kuma ya zabi Peter Obi a matsayin abokin takararsa

- Ya ce Nigeria na bukatar shugaban da zai sake dawo da ita madai-daiciyar hanya

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasar Nigeria karkashin jam'iyyar PDP ya ce idan har aka zabe shi a 2019, to kuwa ba zai dauki tsawon watanni 6 kafin ya bayyana sunayen mukarraban gwamnatinsa ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a ranar da ya zabi Peter Obi a matsayin abokin takararsa, wanda kuma shine tsohon gwamnan jihar Anambra.

Atiku ya kuma jaddada yunkurinsa na zabar mukarraban gwamnatinsa tunma kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, ma damar dai ya lashe babban zaben 2019 da ke gabatowa.

KARANTA WANNAN: Ko kusa Atiku ba zai iya hana Buhari ya zarce a 2019 ba - Dan takarar Sanata

Idan har na zama shugaban kasa: Ba zan dauki watanni 6 kafin bayyana mukarrabaina ba- Atiku

Idan har na zama shugaban kasa: Ba zan dauki watanni 6 kafin bayyana mukarrabaina ba- Atiku
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Atiku ya ce: 'Idan har 'yan Nigeria suka zabeni a matsayin shugaban kasa, ba zan kwashe watanni 6 kafin na bayyana sunayen mukarrabaina ba.

"Zan sanar da mukarrabaina kafin 29 ga watan Mayu, 2019, idan har Allah ya sa an zabe ni a matsayin shugaban kasa. Kasarmu na bukatar shugaban da zai sake dawo da ita madai-daiciyar hanya."

Idan ba'a manta ba, shugaban kasar yanzu, Muhammadu Buhari, ya shafe watanni shida da hawa mulki kafin ya bayyana sunayen mukarraban gwamnatinsa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel