Gaskiyar dalilin da ya sa muka tura jami'anmu kai sumame gidan Dino Melaya - Rundunar 'yan sanda

Gaskiyar dalilin da ya sa muka tura jami'anmu kai sumame gidan Dino Melaya - Rundunar 'yan sanda

- Rundunar yan sanda ta jihar Kogi ta tabbatar da cewar itace ta tura jami'anta zuwa gidan Sanata Dino Melaye da ke Aiyetoro-Gbede a jihar ta Kogi

- Rundunar ta kuma zargi Melaye, da tara 'yan ta'adda don kai farmaki ga jami'anta da ke kan aiki a hanyar Mopa zuwa Aiyetoro

- Rundunar ta gayyaci Melaye a cikin wata wasika mai lamba AR:300/KGS/X/VOL.43/670 mai don zuwa ya amsa tambayoyi amma ya ki zuwa

Biyo bayan zarge zargen da Sanata Dino Melaye ya ke yi na cewar wasu jami'an 'yan sanda sun kai sumame a gidansa, da nufin kawar da shi daga doron duniya, runduanr 'yan sanda ta jihar Kogi, ta mayar mashi da martani kan wannan ikirari.

Rundunar yan sanda ta jihar Kogi ta tabbatar da cewar itace ta tura wasu daga cikin jami'anta zuwa gidan Sanata Dino Melaye da ke Aiyetoro-Gbede a jihar ta Kogi, a ranar 11 ga watan Oktoba, don tabbatar da cewa an cafke shi.

A cikin wata sanarwa a Lokoja, rundunar ta ce ta dauki wannan mataki ne biyo bayan harbin wani jami'inta, Sajen Danjuma Salihu da wasu 'yan ta'adda suka yi a ranar 19 ga watan Yuli, wanda ake kyautata zaton cewa sun aikata hakan da yawun sanatan.

KARANTA WANNAN: Ko kusa Atiku ba zai iya hana Buhari ya zarce a 2019 ba - Dan takarar Sanata

Gaskiyar dalilin da ya sa muka tura jami'anmu kai sumame gidan Dino Melaya - Rundunar 'yan sanda

Gaskiyar dalilin da ya sa muka tura jami'anmu kai sumame gidan Dino Melaya - Rundunar 'yan sanda
Source: UGC

Sanarwar wacce mai magana da yawun rundunar , DSP William Aya ya sanyawa hannu, ta ce rundunar ta zabi mayar da martani la'akari da wani zargi da Melaye yayi a shafinsa na Twitter, a ranar 12 ga watan Oktoba, cewar ADC da gwamna Yahaya Bello na jihar sun tura jami'an 'yan sanda gidansa don kashe shi.

Sanarwar ta kuma zargi Melaye, wanda ke wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattijai ta kasa, da tara 'yan ta'adda don kai farmaki ga jami'anta da ke kan aiki a hanyar Mopa zuwa Aiyetoro a ranar 19 ga watan Yuli, ba tare da 'yan sanda sun ko kula su ba.

Aya a cikin sanarwar ya ce, rundunar ta gayyaci Melaye a cikin wata wasika mai lamba AR:300/KGS/X/VOL.43/670 wacce ke dauke da kwanan wata 23/7/2018 don zuwa ya amsa tambayoyi amma ya yi biris da wannan wasikar, wannan ne ya sa rundunar ta tura jami'anta don cafke shi.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel