Ko kusa Atiku ba zai iya hana Buhari ya zarce a 2019 ba - Dan takarar Sanata

Ko kusa Atiku ba zai iya hana Buhari ya zarce a 2019 ba - Dan takarar Sanata

- Mr Daniel Onjeh, ya jaddada cewa ko kadan ba sa kallon Atiku Abubakar a matsayin wata barazana da zata iya hana Buhari ya zarce a zaben 2019

- Ya kara da cewa a yayin da Buhari ke kara samun lambobin girmamawa saboda yaki da cin hanci, shi kuwa Atiku na samun akasin hakan

- Ya shawarci yan Nigeria da su kaucewa duk wata jita jita da wasu bata garin yan siyasa ka iya yadawa don bata sunan shugaban kasa Buhari

Mr Daniel Onjeh, dan takarar kujerar sanata a mazabar Benue ta Kudu karkashin jam'iyyar APC ya jaddada cewa ko kadan ba sa kallon tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin wata barazana da zata iya hana Buhari ya zarce a zaben 2019.

Onjeh, wanda shine shugaban mahukunta a cibiyar bunkasa ayyuka ta kasa PRODA kuma tsohon shugaban kungiyar dalibai ta kasa NANS, ya bayyana hakan a ranar Juma'a, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

KARANTA WANNAN: Ya zamarwa Buhari da Atiku dole su amince da sakamakon zaben 2019 - Jakan Amurka

Ya kara da cewa a yayin da shugaban kasa Buhari ke kara samun lambobin girmamawa saboda shugabanci na gari, adalci da kuma bin diddigi, shi kuwa Atiku na samun akasin hakan.

Ko kusa Atiku ba zai iya hana Buhari ya zarce a 2019 ba - Dan takarar Sanata

Ko kusa Atiku ba zai iya hana Buhari ya zarce a 2019 ba - Dan takarar Sanata
Source: Depositphotos

Ya yi nuni da cewa kyawawan suffofin Buhari na shugabanci da ake buga misali da su, ya sanya shi samun lambar yabo daga kungiyar hadakar kasashen Afrika a matsayin gwarzo wajen yaki da cinhanci da rashawa.

Ya ce a daya bangaren kuwa, Atiku wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa, kuma mataimakin kwantirola na hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastom), ya fuskanci zarge zarge akan cin hanci da rashawa, babakere dama dulmiyewar dukiyar kasar daga hannunsa.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC

Mr Daniel Onjeh, ya yi nuni da cewar tun hawan shugaban kasa Buhari kujerar mulkin Nigeria, ya mayar da hankali wajen yaki da cin hanci da rashawa, daga darajar noma da ilimi, bunkasa rayuwar talakawa ta hanyoyi da dama, farfado da tattalin arzikin kasar, dama dai daga darajar kasar a idon duniya.

Don haka ya shawarci yan Nigeria da su kaucewa duk wata jita jita da wasu bata garin yan siyasa ka iya yadawa don bata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa ko kadan Atiku ba zai iya zama barazana ga yunkurin Buhari na zarcewa a zaben 2019 ba.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel