An sami hujjar yadda mamlakar Saudiyya ta kashe sanannen dan jarida a kasar Turkiyya

An sami hujjar yadda mamlakar Saudiyya ta kashe sanannen dan jarida a kasar Turkiyya

- Jamal Khashoggi dan asalin Saudiyya ne mai zama a Amurka

- Ana tsammanin Saudiyyar ta kashe shi saboda tone-tonensa

- An neme shi an rasa a bayan da bidiyo ya nuna ya shiga ofishin jakadancin Saudi amma bai fito ba

An sami hujjar yadda mamlakar Saudiyya ta kashe sanannen dan jarida a kasar Turkiyya
An sami hujjar yadda mamlakar Saudiyya ta kashe sanannen dan jarida a kasar Turkiyya
Asali: Facebook

Zarge-zargen cewa kasar Mamlakar Saudiyya mai kama-karya, ta kama kuma ta kashe dan asallin kasarta, wanda ya gudu ya buya a Amurka, tun bayan da Sarki Salman ya dora dansa a karagar jiran gado, inda kuma jaridar Washington Post ta bashi aiki.

An sami hujjar yadda mamlakar Saudiyya ta kashe sanannen dan jarida a kasar Turkiyya
An sami hujjar yadda mamlakar Saudiyya ta kashe sanannen dan jarida a kasar Turkiyya
Asali: Facebook

An dai san Mista Jamal da rubutun sirrukan da ke cikin kasar Saudiyya, musamman irin ta'asar da ake tafkawa da sunan addini ko ta neman kudi a mulki a cikin manyan fadojin kasar.

Sai dai bayan da aka fara kamen masu irin wannan rubutu a kasar, ya tsere zuwa Amurka, inda ya ci gaba da rubutunsa babu kakkautawa, rubutu da ke batawa masu mulkin kasar rai.

DUBA WANNAN: Aljannu dubunnai sun karbi darikar Tijjaniyya

Sai dai, bayan da ya saki matarsa, yake neman kuma ya auri wata, ya shiga ofishin jakadancin kasar a Turkiyya, domin ya sami takardun aurensa da gwamnati ke bayar wa.

Sai dai tun biyu ga wannan wata da ya shiga, shiru babu duriyarsa, watakil, ko an sace shi an kai Saudiyyar, kamar yadda aka saba, ko kuma an kashe shi an yi gunduwa-gunduwa dashi don a batar dashi gaba daya.

Amurka da Turkiyya na bincike, bayan da budurwarsa ta bada wayarsa, wadda ta nuna ashe tun da aka tsare shi ya kunna rikodar dake kan agogonsa na Apple, mai hade da wayarsa, wanda zai bada damar a sami bayanai daga wayar tasa wadda ke hannun babe din tasa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel