NNPC: Masu fasa bututu da satar mai ne suka jawo gobarar bututun jiya - Bincike

NNPC: Masu fasa bututu da satar mai ne suka jawo gobarar bututun jiya - Bincike

- Masu fasa bututu da satar man fetur sun assasa aukuwar gobara

- Barayin man sun fasa bututun ne don datse gudanar mai daga Fatakwal zuwa Aba

- Baru ya nuna damuwarshi akan asarar rayuka da dukiyoyi da gobarar ta jawo

NNPC: Masu fasa bututu da satar mai ne suka jawo gobarar bututun jiya - Bincike

NNPC: Masu fasa bututu da satar mai ne suka jawo gobarar bututun jiya - Bincike
Source: UGC

A jiya ne matatar man fetur ta kasa ta bayyana yanda barayin man fetur suka assasa faruwar gobarar bututun mai dake karshen Osisioma, kusa da Aba.

A jawabin matatar man fetur din ta kasa, daga manajan ta na bangaren kula da harkokin jama'a, Mista Ndu Ughamadu, ya tabbatar da rashin dukiya da rayukan da gobarar ta jawo.

Yace kwararru gurin kiyayewa na matatar man fetur din tare da jami'an kwana kwana na jihar Abia suna gurin don ganin sun shawo kan matsalar.

Ughamadu yace gobarar ta faru ne saboda barayin man fetur din sun fasa bututun mai wanda ya taho daga Fatakwal zuwa Aba.

DUBA WANNAN:Aljannu dubbai sun karbi darikar Tijjaniyya a Hannun Dahiru Bauchi - Rahotanni

Manajan matatar, Mista Maikanti Baru, ya nuna damuwar shi akan rasa rayuka da dukiya da gobarar ta jawo.

Baru ya roki Ubangiji da yaji kan rayukan da aka rasa, tare da jan kunnen mazauna gurin da su guji bata hanyoyin mai da iskar gas saboda da yawan su kan kawo gobara.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel