Ya zamarwa Buhari da Atiku dole su amince da sakamakon zaben 2019 - Jakadan Amurka

Ya zamarwa Buhari da Atiku dole su amince da sakamakon zaben 2019 - Jakadan Amurka

- Wani jakada daga kasar Amurka, McCain ya ce ya zamarwa Buhari da Atiku dama sauran yan takara wajibi su amince da sakamakon zaben 2019

- McCain ya ce amimcewa da sakamakon ne zai hana zubar da jini a kasar

- Ya buga misali akan zaben 2015, wanda aka gudanar ba tare da wadanda suka sha kaye sun ja daga ko tayar da hatsaniya ba

Ya zamarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, da kuma tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, dole su amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 don kaucewa zubar da jini a kasar.

Farfesa Danny McCain, jakadan manyan malamai na duniya, daga kasar Amurka, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma'a a Abuja, ya kara da cewa sakamakon zaben zai haska matsayar jama'ar kasar akan kowacce kuri'a da suka kada.

Ya yi wannan jawabi ne a wani taron lakca karo na 9, mai taken: 'Nigeria a mafarkinmu', taron da wata kungiya mai taken 'Canjin da muke nema a Nigeria' ta shirya.

KARANTA WANNAN: Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC

Ya zamarwa Buhari da Atiku dole su amince da sakamakon zaben 2019 - Jakan Amurka

Ya zamarwa Buhari da Atiku dole su amince da sakamakon zaben 2019 - Jakan Amurka
Source: Facebook

McCain ya ce ya kamata gwamnati ta zage damtse wajen cimma muradun yan Nigeria, wajen hadin kai tsakanin Kirista da Musulmi, walau masu ilimi ko marasa ilimi, ya zamana cewa kowa na aiki ne don cimma mafarkan shuwagabannin da suka samar da kasar har ta samu 'yancinta.

Ya ce yana da yakinin cewa zaben 2019 dai kasance cikin kwanciyar hankli ba tare da an rasa rayukan mutane ba, haka zalika za a gudanar da sahihin zabe ba tare da murdiya ko aringizon kuri'u ba.

"Ya zama wajibi ga yan takarar su amimce da sakamakon zaben, wadanda suka sha kasa, dole su hakura da shan kaye, wadanda suka samu nasara kuwa, su rungumeta da hannu biyu biyu, mun ga dai yadda hakan ta kasance a zaben 2015," a cewarsa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel