Buhari ya bukaci ministansa na sadarwa ya yi murabus

Buhari ya bukaci ministansa na sadarwa ya yi murabus

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsammanin ministansa na harkokin sadarwa, Alhaji Adebayo Shitu, ya yi murabus daga mukaminsa saboda rashin mallakar takardar bautar kasa (NYSC).

Minista Shitu ya ki yin bautar kasa bayan ya kammala karatu daga jami'ar Ife, wacce yanzu ta koma jami'ar Obafemi Awolowo, dake jihar Osun.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai, Shitu, ya bayyana cewar bai samu damar yin bautar kasa bane saboda yana kammala jami'a aka zabe shi a matsayin dan majalisa, aikin da ya ce shi ma na bautar kasa ne.

Bisa dalilin rashin mallakar takardar bautar kasar ne ya saka jam'iyyar APC yin watsi da kudirinsa na son yin takarar gwamna a jihar Oyo.

Sai dai wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa jaridar Punch cewar a jiya, Juma'a, ne shugaba Buhari ya bukaci ministan da ya yi abinda ya dace.

Buhari ya bukaci wani ministansa ya yi murabus

Buhari da Shittu
Source: Depositphotos

Majiyar ta kara da cewar Buhari ya fadawa ministan baro-baro cewar bai kamata ya tsaya jiran har sai ya bukaci ya yi magana ba kafin ya ajiye mukaminsa.

"Maganar gaskiya shugaba Buhari ya bukaci ministan ya ajiye mukaminsa, kuma mu shaida ne.

"Shugaba Buhari ya yi korafin cewar bai kamata a ke jiran sai ya yi magana kafin wani daga cikin hadimansa ya yi abinda ya dace," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Fallasa: Hadimar shugaba Buhari ta tonawa shugaba CAN asiri a kan yawan sukar shugaban kasa

Ko a kwanakin baya sai da shugaba Buhari ya bukaci ministar sa ta kudi, Kemi Adeosun, ta ajiye mukaminta bayan ta yi karyar mallakar takardar bautar kasa.

Ba a samu damar jin ta bakin masu magana da yawun shugaban kasa; Garba Shehu da Femi Adesina, a kan wannan batu saboda wayoyinsu a kashe su ke har zuwa yammacin juma'a da jaridar Punch ta wallafa wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel