Rainin wayo: Wasu masu safarar mutane biyu sun tsere daga hannun hukuma

Rainin wayo: Wasu masu safarar mutane biyu sun tsere daga hannun hukuma

- Wasu mutane biyu da ake zargi da laifin safarar kananan yara sun tsere daga hannun hukumar NAPTIP

- An gano cewar wasu jami'an hukumar ne suka taimaka musu wajen tserewar kuma tuni an sallame su daga aiki

- A halin yanzu hukumar ta bazama nemansu kuma tana rokon jama'a su taimaka da bayanai da zai sanya a gano inda suke

Wasu mutane biyu da ake zargi da laifin safarar mutane, Linus Okeke da Godwin Nomyange da Hukumar Yaki da Masu Safarar Mutane na kasa (NAPTIP) da kama sun tsere daga hannun hukumar a jihar Legas.

Bincike ya nuna cewar wasu jami'an hukumar yaki da masu safarar mutane ne suka taimaka wa wadanda ake zargin suka tsere makonni biyu da suka gabata.

Rainin wayo: Wasu masu safarar mutane biyu sun tsere daga hannun hukuma

Rainin wayo: Wasu masu safarar mutane biyu sun tsere daga hannun hukuma
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Hanyoyi 6 da ake amfani da goro da ya dace ku sani

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar an kama mutane biyun ne saboda ana zarginsu da safarar wasu kananan yara biyu kuma ana gudanar da bincike ne kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.

Mai magana da yawun hukumar, Mrs Stella Nezan ta tabbatar tserewar wanda ake zargin ta kuma kara da cewar tuni hukumar ta sallami jami'an da suka taimaka wa masu laifin suka gudu kuma suma za a gurfanar da su a kotu.

Ta ce hukumar ta NAPTIP ta baza jami'anta a duk sassan kasar nan domin kamo wadanda suka tsere daga hannun hukumar.

"Direkta Janar na NAPTIP, Julie Okah-Donli ya na kira ga dukkan al'umma su taimaka wa hukumar da duk wani bayani da zai taimaka wajen kamo wadanda suka tsere domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su," inji Nezan.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel