Allah ne ya zabi Atiku domin ceto Najeriya daga Buhari - Osuntokun

Allah ne ya zabi Atiku domin ceto Najeriya daga Buhari - Osuntokun

Mista Akin Osuntokun, kakakin jam'iyyar CNM, Coalition for Nigeria Movement, ya bayyana cewa nasarar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin tsayayyen dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wani zabi daga Mahalicci mai kowa mai komai.

Osuntokun ya bayyana cewa, Atiku wani zababben tafarki ne na Mai Duka domin ya ceto Najeriya daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya misalta shi a matsayin madawwamin duhu mai tsananin gaske.

Kakakin jam'iyyar cikin jawabansa a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, aminci da kuma goyon tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ga Atiku wani babban yunkuri ne na ceto kasar nan tare da kai ta ga Tudun tsira.

Yake cewa, yunkurin Obasanjo bayan sun hau kan shafi guda da Atiku na sulhu ya bayu da tsarkakakkiyar manufa ta ajiye sabanin ra'ayi a gefe guda domin cimma manufa daya ta inganta kasar nan da kuma bunkasar ta.

Allah ne ya zabi Atiku domin ceto Najeriya daga Buhari - Osuntokun

Allah ne ya zabi Atiku domin ceto Najeriya daga Buhari - Osuntokun
Source: Depositphotos

Ya ci gaba da cewa, nasarar Atiku a matsayin dan takara da zai ja daga da Buhari a zaben 2019 wani zabi da Mai Duka ya danka a hannun al'ummar kasar nan da za su kada masa kuri'u domin ceto Najeriya daga ibtila'i da ta ke fuskanta karkashin jagorancin shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: 'Yan Majalisar tarayya 272 da ba bu lallai su koma kujerun su a 2019

Mista Osuntokun ya yi kira kan ajiye bambance-bambance na ra'ayi a gefe guda domin cimma manufa daya ta ceto kasar nan da a halin yanzu takarar Atiku wata hikima ce ta Mai Duka da zai fidda A'i daga Rogo.

Kazalika jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a jiya Juma'a jam'iyyar APC ta kasa ta nada Alhaji Lanre Issa, a matsayin sabon kakaki da zai ci gaba da rike mukamin mai magana da yawun ta.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel