Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta nada sabon kakakin ta

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta nada sabon kakakin ta

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta nada Alhaji Lanre Issa a matsayin sabon kakakin ta ko kuma ace mai magana da yawun ta.

Duk da dai cewa jam'iyyar ta APC bata bayyana nadin ba a hukumance amma dai majiyar mu ta Premium Times ta bayyana mana cewa shi wanda aka nada din shine ya shaida masu tabbacin nadin.

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta nada sabon kakakin ta

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta nada sabon kakakin ta
Source: Facebook

KU KARANTA: Sarki Sanusi ya soki gwamnonin Arewa

Legit.ng dai ta samu cewa jam'iyyar ta APC bata da mai magana da yawun ta na din-din din tun bayan da Mista Bolaji ya fice daga jam'iyyar a watannin baya wanda kuma daga baya aka nada Mista Yekini Nabena a matsayin kakaki na wucin gadi.

A wani labarin kuma Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta zargi tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da shiga gaba tare da yin kutun-kutun wajen ganin kasar Amurka ta yafewa tsohon mataimakin sa, Atiku Abubakar laifin sa.

Jam'iyyar ta APC ta ce ta samu wannan bayanan ne na sirri daga wasu makusantan na tsohon shugaban kasar wanda a ranar Larabar da ta gabata ne suka yi sulhu da mataimakin nasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zaben 2019 mai zuwa.

Wannan dai ikirarin na jam'iyyar ta APC na kunshe ne a cikin wata sanarwar da maimagana da yawun ta Mista Yekini Nabena ya sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel