Da dumin sa: Gwamna Fayose ya hannunta takardun barin gwamnatin sa

Da dumin sa: Gwamna Fayose ya hannunta takardun barin gwamnatin sa

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya mika takardun barin gwamnatin sa zuwa ga shugaban ma'aikata na jihar Dakta Gbenga Faseluka da daren yau kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu da dama.

Mun samu cewa gwamnan dai ya mika takardun na barin aikin nasa ne a yayin wani taron majalisar zartarwar jihar na musamman da ya shugabanta yau da ya samu halartar wau daga cikin sarakunan gargajiyar jihar.

Da dumin sa: Gwamna Fayose ya hannunta takardun barin gwamnatin sa

Da dumin sa: Gwamna Fayose ya hannunta takardun barin gwamnatin sa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Sarki Sanusi ya yiwa gwamnonin Arewa wankin babbab bargo

Legit.ng ta samu cewa da yake jawabi kafin mika takardun, gwamnan Fayose ya roki al'ummar jihar da ma kasa baki daya da su yafe masa dukkan kura-kuran da ya yi a lokacin da yana gwamnan jihar.

Haka zalika ya kuma sha alwashin tsayawa ya ansa dukkan tambayoyin da za'a yi masa game da gwamnatin tasa daga kowa.

A wani labarin kuma, Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta zargi tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da shiga gaba tare da yin kutun-kutun wajen ganin kasar Amurka ta yafewa tsohon mataimakin sa, Atiku Abubakar laifin sa.

Jam'iyyar ta APC ta ce ta samu wannan bayanan ne na sirri daga wasu makusantan na tsohon shugaban kasar wanda a ranar Larabar da ta gabata ne suka yi sulhu da mataimakin nasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zaben 2019 mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel