Atiku ya zolaye Buhari a kan nadin ministoci

Atiku ya zolaye Buhari a kan nadin ministoci

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zolaye shugaba Muhammadu Buhari kan jinkirin nadin ministoci

- Atiku ya ce idan 'yan Najeriya suka zabe shi zai nada ministocinsa kafin ranar 29 ga watan Mayun 2019

- Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashe watanni shida kafin ya nada ministocinsa a Nuwamban 2015

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya yi alkawarin zai zabi ministocinsa kafin a rantsar da shi kan mulki mudin ya lashe zaben shugabancin kasa na 2019.

Atiku ya yi wannan furucin ne domin zaulayar shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce idan aka zabe shi zai nada ministocinsa kafin 29 ga watan Mayun shekarar 2019.

Atiku ya zoleye a kan nadin ministoci

Atiku ya zoleye a kan nadin ministoci
Source: Twitter

"Idan 'yan Najeriya suka zabe ni a matsayin shugaban kasa, ba zan dauki watanni 6 ba kafin nada ministoci na. Zan zabi ministoci na kafin 29 ga watan Mayu da izinin Allah. Najeriya na bukatar shugaba mai daukan mataki kan lokaci," kamar yadda Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter.

DUBA WANNAN: Abinda Obasanjo ya fada min cikin sirri kafin ya goyi baya na - Atiku

Idan ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari dai an rantsar da shi ne a ranar 29 ga watan Mayun 2015 amma bai nada ministocinsa ba sai watanni bayan watanni 6 a cikin watan Nuwamba.

Masu nazarin al'amurran siyasa da dama sun ce rashin nadin ministocin kan lokaci na daya daga cikin abubuwan da suka kara janyo tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya a farkon mulkin Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel