Baki-abun-magana: Sarki Sanusi yayi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya

Baki-abun-magana: Sarki Sanusi yayi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya

Sarkin masarautar Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya game da daukar dukiyar al'umma da sukeyi suna anfani da ita wajen biyawa wasu tsiraru kujerar Makka duk shekara.

Sarkin yayi wannan tsokacin ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bita na lalubo hanyoyin da za'a rage yawan yaran da basu zuwa makaranta a yankin na Arewacin Najeriya da aka kammala a ranar Alhamis.

Baki-abun-magana: Sarki Sanusi yayi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya

Baki-abun-magana: Sarki Sanusi yayi kaca-kaca da gwamnonin Arewacin Najeriya
Source: UGC

Sarki Sanusi yace ko kusa biyawa talakan da bai da hali kudin zuwa Makka ba daidai bane domin bata wajaba a kan sa ba to balle kuma ma a dauki kudin al'umma a biya masu.

Daga karshe ya kuma shawarci gwamnatin na Arewacin Najeriya da su maida hankalin su wajen habaka harkar ilimi da lafiyar al'umma ba kankanba da karambani ba.

A wani labarin kuma, Kwamitin nan na musamman da Shugaba Buhari ya kafa domin kwato kadarorin gwamnati dake a hannun ma'aikatan gwamnati ya ce ya samu nasarar kwato akalla Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati.

Shugaban kwamitin da aka dorawa alhakin kwato kadarorin, Mista Okoi Obono-Obla shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishin sa a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel