El-Rufa’I da Uba Sani na shirin kulla min sharrin cin hancin N10m – Shehu Sani

El-Rufa’I da Uba Sani na shirin kulla min sharrin cin hancin N10m – Shehu Sani

Shehu Sani, sanatan da ke wakiltan mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya kawo kuka kan wani tuggu da gwamnan jihar Kaduna ke kokarin shirya masa cewa ya bada cin hancin N10million.

Ya bayyana hakan ne a wata jawabi da ya saki ta bakin mai basa shawara kan harkokin siyasa, Kwamred Suleiman Ahmed, a yau Juma’a 12 ga watan Oktoba a birnin tarayya Abuja.

Jawabin yace: “An jawo hankalin Sanata Shehu Sani kan wani sabon kaidin da ake shirya masa kumaa shugaban kwamitin zaben fidda gwanin sanatan Kaduna ta tsakiya ke yadawa.

Kana gwamnatin jihar Kaduna ke hura wutan zargin cewa Shehu Sani ya baiwa shugaban kwamitin cin hancin N10m ta hannun wani amma bai amsa ba. Babu gaskiy cikin wannan magana, karya ce zalla.”

"Sanata (Shehu Sani) ya bayyana karara tun kafin zaben bogin da suka gudanar cewa ba zai yi musharaka cikin zaben ba saboda ya sabawa ka’idojin jam’iyyar da kuma karan da abokin gwamnan Uba Sani ya shigar kotu.”

KU KARANTA: Fuskoki da sunayen masu garkuwa da mutane 16 da yan sanda suka kama

Mun kawo muku rahoton cewa Mukaddashin Sakataren yada labarai na APC na kasa baki daya Yekina Nabena ya musanya cewa an ba wasu da su ka lashe zaben fitar da gwani satifiket. Nabena ya karyata wannan ne lokacin da ya zanta da manema labarai jiya.

A jawabin da Yekina Nabena yayi, za a fahimci cewa rikicin Jam’iyyar game da kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya wanda Shehu Sani yake kai yanzu ya sake daukar wani salo bayan Jam’iyyar tace ba ta ba kowa shaidar nasara ba.

A baya dai ana ta yada cewa Jam’iyyar APC ta mikawa Uba Sani satifiket a matsayin shaidar lashe zaben fitar da gwani. Nabena yace babu gaskiya a lamarin domin Jam’iyyar mai mulki ba ta kowa wani satifiket a kaf Najeriya ba.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel